A Karshe Tinubu Ya yi Magana a Kan Shirin Maida Legas Ta Koma Birnin Tarayya

A Karshe Tinubu Ya yi Magana a Kan Shirin Maida Legas Ta Koma Birnin Tarayya

  • Kwamitin yakin neman zaben Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya karyata maganar canza birnin tarayya
  • Bayo Onanuga wanda shi Darektan yada labarai da hulda da jama’a na kwamitin takaran ya fitar da jawabi
  • Onanuga yace ana neman bata ‘dan takaransu, amma Tinubu ba zai maida birnin tarayya zuwa Legas ba

Abuja - Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya musanya rade-radin da ke yawo na shirin canza birnin tarayyan Najeriya.

The Nation tace ana jita-jita idan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zama shugaban kasa, babban birnin tarayyan zai koma Legas a maimakon Abuja.

Kwamitin neman takaran Bola Tinubu ya fitar da jawabi da ya karyata wannan batu, yace ‘yan adawa ke yada wannan domin su bata ‘dan takaransu.

Jawabin ya fito ta bakin Darektan yada labarai da hulda da jama’a na kwamitin APC, Bayo Onanuga.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Tafi Amurka da Kasashen Turai, An Samu Bayanin Abin da Zai Kai Shi

Bayo Onanuga yake cewa tsohon gwamnan na jihar Legas kuma ‘dan takaran shugaban kasa a 2023 ba zai yi tunanin abin da ya saba doka ba.

Jawabin Bayo Onanuga

"Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, yana ankarar da ‘Yan Najeriya game da sharrin da ake yi wa ‘dan takaranmu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a wasu yankunan kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu.
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Daga cikin karyayyakin da ake yadawa, musamman a bangaren Arewa maso yammacin kasar nan shi be Tinubu yana da niyyar dauke birnin tarayya daga Abuja zuwa Legas idan ya gaji Muhammadu Buhari.

Aikin 'Yan PDP ne - PDP PCC

Daily Trust ta rahoto Onanuga yana cewa a masu yada labarin akwai tsofaffin da ke tare da PDP.

Kwamitin yace ya yi mamakin jin yadda ake sharara karya da sunan siyasa. Darektan ya tabbatar da cewa Abuja zai cigaba da zama babban birni.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Jingine Siyasa, Ya Bayyana Mutumin Da Ya Cancanci Zama Shugaban Kasa a 2023

A cewarsa, ba wannan ne karon farko da aka yi irin haka ba, an yi ta surutai a kan batun sa NNPC a kasuwa da shawarar da Atiku Abubakar ya kawo.

An kama Ogan Boye

An ji labari ana tsoron jami'an tsaro sun je gida sun dauke Yusuf Imam, wanda daya ne daga cikin masu taimakawa New Nigeria People’s Party a Kano.

Ogan boye ya nemi takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar NNPP, kuma yana cikin wadanda suka matsa lamba ga jam’iyyar APC mai rike da mulki

Asali: Legit.ng

Online view pixel