Tinubu Zai Tafi Amurka da Kasashen Turai, An Samu Bayanin Abin da Zai Kai Shi

Tinubu Zai Tafi Amurka da Kasashen Turai, An Samu Bayanin Abin da Zai Kai Shi

  • A Disamba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai kai muhimman ziyara zuwa wasu kasashen ketare
  • ‘Dan takaran shugaban kasar na All Progressives Congress zai je Amurka, Landan, da irinsu Faransa
  • Bola Tinubu zai tallata manufofinsa a gaban shugabannin Duniya domin samun goyon bayansu

Abuja - ‘Dan takaran shugaban kasar Najeriya a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yana shirye-shiryen barin Najeriya zuwa ketare.

Wani rahoto da aka samu a Daily Trust a ranar Litinin, 28 ga watan Nuwamba 2022, ya nuna ‘dan takaran na zaben 2023 zai ziyarci kasar Amurka.

Baya ga Amurka, Bola Ahmed Tinubu zai yi amfani da damar domin shiga kasashen Turai.

Wadannan bayanai sun fito ne daga kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a 2023 a shafinsu na Twitter a farkon makon nan.

Kara karanta wannan

Jihar Kano Da Wasu Jihohin Arewa 5 Da Nike Da Tabbacin Zan Lashe: Tinubu

4 ga wata zuwa 12 ga wata

A wannan tafiya zuwa kasashen waje, Bola Tinubu zai yi nasarar ganawa da shugabannin Duniya, kuma ya tallata takarar shugaban kasa da yake yi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga ranar 4 ga watan Disamban 2022 ne Tinubu zai tafi manyan Biranen kasashen yamma, ana sa rai zai shafe fiye da mako daya kafin ya dawo gida.

Tinubu
Bola Tinubu a Legas Horo: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Zuwa ranar 14 ga watan na Disamba ‘dan takaran zai cigaba da yawon yakin zama shugaban kasa da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki a zabe.

Tawagar Bola Tinubu za ta je Landan (Birtaniya), Amurka, Faransa da kuma wasu muhimman kasashen da ke cikin karkashin kungiyar nahiyar Turai.

Sanarwar take cewa Tinubu zai saida manufofinsa ga kasashen yammacin Duniyan, kuma ya nemi goyon bayan na su wajen zama shugaban Najeriya.

Burin zama Magajin Buhari

Kara karanta wannan

2023: Tun da ‘Dan takaransa ya sha kashi, Buratai ya nuna wanda yake goyon baya

Burin Tinubu shi ne a watan Mayun 2023, ya gaji Mai girma Muhammadu Buhari wanda yake rike da ragamar shugabancin Najeriya tunkarshen 2015.

A Landan, jam’iyyar APC tace Tinubu zai yi jawabi a kan sha’anin tsaro da manufofinsa na huldatayyar kasa da kasa a dakin taron Chatham House.

Ganin yadda kasasen yamma suke da karfi a Afrika, ‘dan takaran zai hadu da masu juya akalarsu.

Rikici a Jam'iyyar LP

An samu rahoto cewa a jam'iyyar LP, ‘dan takaran shugaban kasa, shugaban jam’iyya, shugaban kwamitin zabe da sakataren PCC duk daga Kudu suka fito.

Hakan ya jawo wasu suka fara Allah-wadai da yadda ake nunawa ‘Yan siyasan yankin Arewa son kai alhali Najeriya ta kowa ce, suka bukaci ayi gyara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel