Dakarun ‘Yan Sanda Sun Kama Wani Babban Jagoran Jam’iyyar NNPP a Kano

Dakarun ‘Yan Sanda Sun Kama Wani Babban Jagoran Jam’iyyar NNPP a Kano

  • Ana tunanin ‘yan sanda sun dauke daya daga cikin kusoshi a jam’iyyar NNPP na reshen jihar Kano
  • Rahoto ya nuna an dauke Amb. Yusuf Imam wanda mutane suka fi sani da Ogan Boye daga gidansa
  • Rikicin siyasa ya barke tsakanin magoya bayan New Nigeria People’s Party da All Progressives Congress

Abuja - Ana zargin wani daga cikin kusoshin jam’iyyar NNPP a jihar Kano, Amb. Yusuf Imam ya shiga hannun rundunar ‘yan sandan Najeriya.

Jaridar Sahelian Times ta rahoto cewa ‘yan sanda sun kama Yusuf Imam wanda aka fi sani da Ogan Boye. Abin ya faru ne dai a farkon makon nan.

Idan ta tabbata, jami’an ‘yan sanda sun kama Ogan Boye ne a gidansa da ke karamar hukumar Nasarawa, daga nan suka kai shi ofishinsu a Bompai.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Zulum Ya Sha Alwashin Hana ‘Yan Adawa Samun Nasarar Komai a Borno

Har yanzu ba a bada dalilin da ya sa aka kama Imam ba, amma rahoton ya nuna hakan bai rasa nasaba da rikicin siyasar da ake fama da ita a Kano.

Meyasa aka kama Ogan boye?

An yi yunkurin tuntubar kakakin ‘yan sanda na reshen jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, amma ba a iya samunsa a wayar salularsa ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A ‘yan kwanakin bayan nan ana ta samun sabani tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki da kuma ‘yan bangaren jam’iyyar NNPP mai hamayya.

Jigo a Jam’iyyar NNPP a Kano
Jigo a NNPP, Yusuf Imam Hoto: @ambyusuf.oganboye
Asali: Facebook

Magoya bayan APC da na NNPP sun yi fada a yankin Nasarawa, inda mataimakin Gwamna kuma ‘dan takaran Gwamnan Kano a APC a 2023 ya fito.

Shi ma Yusuf Imam watau Ogan Boye ya fito daga wannan yanki ne, This Day tace yana cikin masu taimakawa NNPP wajen yakar jam’iyya mai mulki.

Kara karanta wannan

LP Ta Batawa Atiku Lissafi, Shugaban PDP Yana Goyon Bayan a Zabi Peter Obi

An yi irin wannan rigingimu a Charanci a karamar hukumar Gwale, yankin ‘dan takaran NNPP, Abba Kabir Yusuf da shugaban APC, Abdullahi Abbas.

Ko da tsiya - ko tsiya-tsiya

Bayan Abdullahi Abbas ya sake nanata cewa ko da tsiya ne, jam’iyyar APC sai ta ci zabe a 2023, jam’iyyar ta NNPP ta reshen Kano maida masa martani.

Shugaban NNPP a Kano, Umar Haruna Doguwa yace idan har goron gayyata ne shugaban na APC ya aika masu, to sun karbi tayin neman rigima su.

Borno ta APC ce - Zulum

Bayan tsawon kwanaki ana musanya lamarin, an ji labari Farfesa Babagana Umara Zulum ya ba Atiku Abubakar hakurin harin da aka kai wa ‘Yan PDP.

Gwamnan ya fadawa jam’iyyun adawa bai jin tsoronsu, kuma su daina sa rai za su iya lashe wata kujera a zaben da za a shirya a farkon shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Kaddamar da Gangamin Kamfen din APC a Gaya

Asali: Legit.ng

Online view pixel