Jam'iyyar APC Ta Bayyana Sahihancin Dakatarwar da Aka Sake Yi Wa Ganduje

Jam'iyyar APC Ta Bayyana Sahihancin Dakatarwar da Aka Sake Yi Wa Ganduje

  • Jam'iyyar APC a jihar Kano ta fito ta sake yin magana kan batun sake dakatar da Abɗullahi Umar Ganduje daga jam'iyyar
  • Sakataren APC na jihar ya bayyana cewa waɗanda suka sanar da sake dakatar da Ganduje ba halastattun ƴaƴan jam'iyyar ba ne
  • Ya bayyana su a matsayin ƴan siyasa da suka sayar da mutuncinsu domin samun abun duniya, sannan ya buƙaci jama'a da su yi watsi da dakatarwar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Jam'iyyar APC reshen jihar Kano, ta buƙaci jama’a da su yi watsi da batun dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Sakataren jam’iyyar a jihar, Alhaji Zakari Sarina, shi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, 22 ga watan Afirilun 2024.

Kara karanta wannan

Masu ruwa da tsaki a APC sun goyi bayan dakatar da Ganduje, sun buƙaci abu 1

APC ta magantu kan dakatar da Ganduje
Jam'iyyar APC ta yi fatali da batun sake dakatar da Ganduje Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta ambato sakataren na APC na cewa dakatarwar da wasu gungun mutane suka yi wa Ganduje, ba ta da amfani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me APC ta ce kan dakatarwar Ganduje?

Ya ce dakatarwar wacce wani ɓangare na jam’iyyar ya sanar a ranar Lahadi, ta fito ne daga waɗanda ba ƴaƴan jam’iyyar ba, rahoton jaridar PM News ys tabbatar.

"Ba abu ba ne mai yiwuwa waɗanda ba ƴaƴan jam'iyya ba su dakatar da mutumin da yake da muƙami a uwar jam'iyya ta ƙasa ba tare da bin ƙa’ida ba kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada."
"Dole ne na bayyana cewa, ayyukan waɗannan sojojin gonan bai dame mu ba saboda sun nuna cewa ba su san inda suka dosa ba, kuma ya ƙara fallasa rashin iya siyasarsu a fagen da Abdullahi Umar Ganduje ya zama ubangida."

Kara karanta wannan

Dakatar da Ganduje karo na biyu: APC ta mayar da martani mai zafi ga 'yan tawaren jam'iyyar

"Daga bayanan da muke da su, waɗanda ke bayan wannan sabon rashin gaskiyan wasu ƴan siyasa ne da suka sayar da mutuncinsu saboda abin duniya."

- Alhaji Zakari Sarina

Masu dakatarwar ba ƴan APC ba ne?

A cewarsa ba ƴaƴan jam'iyyar ba ne domin mamba nagari na jam'iyyar ba zai so ya lalata halastaccen ɗan jam'iyya wanda ya yi gwamna na shekara takwas sannan ya kai matakin shugaban jam'iyya na ƙasa ba.

Sarina ya yi zargin cewa shugaban ƴan tawagar da suka sanar da dakatar da Ganduje, ɗan jam'iyyar NNPP ne wanda ya yi takarar Kansila a mazaɓar Ganduje amma bai samu nasara ba.

Ƴan APC sun koma NNPP a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴaƴan jam'iyyar APC sama da mutum 1000 sun tattara kayansu sun fice daga jam'iyyar a jihar Kano.

Tsofaffin mambobin na jam'iyyar APC sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar NNPP mai mulkin jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel