Gwamnatin El-Rufai Ta Ci Tarar N1m a Kan APC, PDP Saboda Fostocin ‘Yan Takara

Gwamnatin El-Rufai Ta Ci Tarar N1m a Kan APC, PDP Saboda Fostocin ‘Yan Takara

Shugaban hukumar KCTA ya rubuta wasika zuwa ga jam’iyyar APC a kan saba dokar lika fostocin takara

Hukumar KCTA tayi alkawarin hukunta ‘yan siyasar da ke bata birnin Kaduna da hotunan masu neman zabe

A dalilin wannan, Muhammad Hafiz Bayero ya yankewa APC da kuma PDP na rassan jihar Kaduna tara

Kaduna - Hukumar KCTA mai kula da raya birnin Kaduna ta aika takarda zuwa ga shugaban jam’iyyar APC, tana cin sa tara a dalilin fostocin ‘yan takara.

Shugaban KCTA, Muhammad Hafiz Bayero ya aika takarda zuwa ga shugaban jam’iyyar APC na reshen Kaduna, yana sanar da shi matakin da ya dauka.

Legit.ng Hausa ta samu ganin wannan wasika mai lamba KCTA/DAF/GC/22/79/VOL 1 da aka fitar tun a watan Oktoban 2022, kuma ya shiga hannun APC da PDP.

Kara karanta wannan

Jigon Siyasa Ya Hango Faɗuwar Atiku da Tinubu, Ya Faɗi Ɗan Takarar Da Zai Gaji Buhari a 2023

Kafin a buga gangunan siyasar 2023, Muhammad Hafiz Bayero ya gargadi jam’iyyu a kan daura fostocin takara gadoji, shatale-tale da irinsu kan fitulun hanya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

KCTA tayi alkawarin cewa za a hukunta duk wata jam’iyya ko ofishin ‘dan takara da ya sabawa wannan doka, ya yi tallar fatsoci a duk wuraren da suka haramta.

A takardar da ya aikawa APC da PDP, shugaban na KCTA yace doka tana aiki har yanzu, don haka ayi amfani da allo, ledoji da kananan takardu wajen talla.

Takardar tarar KCTA
Takardar tarar KCTA Hoto: Abdul Haleem Ringim @abdulhaleem.ishaq.
Asali: Facebook

Hafiz Bayero yace hukumar da yake jagoranta ta lura ‘yan siyasa sun bata wurare da hotuna da fastocin ‘yan takaran 2023, wanda hakan ya ci karo da doka.

A dalilin haka, KCTA tace za ta gyara barnar da masu neman kujerun siyasa suka yi wa wuraren amfanin jama’a, don haka aka ci jam’iyyun nan tarar kudi.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: Buhari Ya Kiyaye, ‘Yan APC Dinsa Na Neman Bata Masa Suna a Ofis

Mun fahimci APC mai mulki a jihar Kaduna da PDP za su biya Naira miliyan 1 asusun gwamnati saboda kunnen kashi da ‘yan takararta suka yi wa hukumar.

Idan har ba a biya wadannan kudi ba, hukumar tace za ta shigar da karar jam’iyyun a kotu.

Kamar yadda Hafiz Bayero ya yi bayani a takardar, muddin aka samu wanda ake tuhuma da laifi a kotu, za a iya yanke masa hukuncin dauri a gidan maza.

Majiyarmu ta shaida mana hukumar ta aika takardar gargadi kafin a kai ga haka.

PDP za ta ci Ribas, Wike

An samu labari Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike yayi hasashen galaba a duka kujerun majalisar dokoki, majalisun wakilai, Sanatoci, da na Gwamna.

Amma kuma Mai girma Gwamnan yace sai an yi gyara kafin PDP ta ci zaben Shugaban kasa a jihar Ribas, alamar bai tare da Atiku Abubakar har yau.

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu Ya Shigar da Karar Gwamnatin Buhari, Yana Neman a Biya Shi N100bn

Asali: Legit.ng

Online view pixel