Dabarar da Atiku Zai bi, Ya Karbo Kudin da Aka Sace a Najeriya Inji Ologbondiyan

Dabarar da Atiku Zai bi, Ya Karbo Kudin da Aka Sace a Najeriya Inji Ologbondiyan

Atiku Abubakar mai neman zama shugaban kasa a Najeriya ya alwashin yakar rashin gaskiya

Kola Ologbondiyan ya yi amfani da bakin ‘Dan takarar PDP, ya ci masa albasa da aka yi hira da shi

Ologbondiyan yace muddin Atiku ya samu mulki, zai bukaci barayi su dawo da abin da suka wawura

Abuja - Kola Ologbondiyan mai magana da yawun bakin Atiku Abubakar, yace ‘dan takaransu zai yi maganin sata da ‘yan siyasar kasar nan suke yi.

Da aka yi hira da shi a gidan talabijin Arise TV a ranar Talata, Kola Ologbondiyan yace Atiku Abubakar zai nemi barayi su dawo da abin da suka sace.

An tambayi Ologbondiyan a kan yadda Alhaji Atiku Abubakar zai yaki rashin gaskiya, sai ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa zai magance lamarin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Tinubu Ya Yi Watsi da Kwankwaso, Ya Fadi Manyan Yan Takara Uku da Zasu Fafata a 2023

Idan Atiku Abubakar ya zama shugaban Najeriya, zai fadawa ‘yan siyasar da ake zargin sun yi sata a Najeriya, “ku dawo da dukiyoyin da kuka sata.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kakakin ‘dan takaran yace irin wannan dabara gwamnatin Obasanjo tayi amfani da shi tsakanin 1999 da 2007 wajen karbo kudin da ke hannun barayi.

Mataimakin shugaban kasa a wancan lokaci shi ne Atiku Abubakar. Rashin gaskiya da satar dukiyar al’umma na cikin matsalolin da ke addabar kasar.

Atiku
Atiku Abubakar a Bayelsa Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

“Ina mai tabbatarwa ‘Yan Najeriya cewa idan aka zabe shi a 2023, Atiku yace zai rage rashin gaskiya da ake yi a kasar nan.
Har ta kai yana cewa idan aka samu mutum da laifin rashin gaskiya da cin amana, za a kira shi, a ce ya dawo da abin da ya dauka.
Ya bada misali da gwamnatin Olusegun Obasanjo, yace mutanen da suka sace kudi, sun dawo da abin da suka dauka a lokacin."

Kara karanta wannan

Dino Melaye Ya Saki Bidiyon Atiku Yana Shakatawa, Ya Karyata Cewa Jinya Ya Tafi Faransa

- Kola Ologbondiyan

The Cable ta rahoto Ologbondiyan yana cewa ba zai tuna nawa gwamnatin PDP ta karbe daga hannun barayi, amma shakka-babu kudi sun dawo Baitul-mali.

"Ba zan iya tuna adadin da ya fada sun karbe a gwamnatin nan ba, amma shakka babu, an dawo da kudi."

- Kola Ologbondiyan

Barazanar LP a 2023

Dazu kun samu rahoto cewa ‘Dan takarar Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi zai iya yin nasara a wasu jihohin da Atiku Abubakar ne ya yi nasara a 2019.

Hasashenmu ya nuna a zaben 2023, ‘Dan takarar PDP watau Atiku zai iya samun kalubale a irinsu Anambra, Ribad da jihar Benuwai daga wajen Peter Obi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel