NNPP Mai Kayan Marmari Zata Lallasa APC, PDP a Zaben Shugaban Kasa 2023, Kwankwaso

NNPP Mai Kayan Marmari Zata Lallasa APC, PDP a Zaben Shugaban Kasa 2023, Kwankwaso

  • Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar NNPP, Rabiu Kwankwaso, yace jam'iyyarsa zata ba da mamaki a zaben 2023
  • Tsohon gwamnan jihar Kano yace da zaran ya dare kujarar shugaban kasa, kowane dalibi zai koma Makaranta
  • Yayin bude Ofishin Kamfen dinsa a Kano, mutane sun yi cikar kwari tun kafin isowarsa suna rera sunansa

Kano - Mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar NNPP mai kayan marmari, Rabiu Musa Kwankwaso, yace jam'iyyarsa zata kifad da APC da PDP a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Daily Trust ta ruwaito cewa Kwankwaso ya faɗi haka ne a Kano yayin da yake jawabi ga dandazon mutane a wurin buɗe Ofishin Kamfen ɗinsa a hukumance.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
NNPP Mai Kayan Marmari Zata Lallasa APC, PDP a Zaben Shugaban Kasa 2023, Kwankwaso Hoto: @SaifullahiHassan
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan yace, "Wannan taron mutanen ya nuna asalin bukatar canza shugabanni ba wai a jihar Kano kadai ba har da kasa baki daya."

Kara karanta wannan

Ta Fasu: Kalaman da Tinubu Ya Nemi Tawagar Matan APC Su Faɗa Wa 'Yan Najeriya Masu Neman Canji a 2023

"Babban abun mamaki na nan tafe a lokacin da jam'iyyar mu NNPP zata laahe zaɓen shugaban ƙasa na 2023 da ikon Allah."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ɗalibai zasu koma makaranta - Kwankwaso

Tsohon Sanatan Kano ta tsakiya, Kwankwaso ya kara da cewa zuwa 2023, kowane ɗalibi zai dara kuma ya samu damar komawa makaranta.

Yace, "Waɗanda ya kamata ace suna Makarantar Firamare daga cikinku zasu koma aji yayin da zaƙaƙurai daga cikinku zamu tura su Jami'o'in kasashen waje."

Tun da farko dai, mutane sun yi cikar kwari, magoya bayan jam'iyyar NNPP, 'yan kasuwa, sanannun yan wasan kwaikwayo duk suka jure wa tsananin rana yayin da suke jiran isowar jagora, Kwankwaso, suna rera sunansa a bakunansu.

Legit.ng Hausa ta zanta da wani ɗan tafiyar Kwankwasiyya wanda ya halarci wurin taron a Kano, Saidu Abdu, yace yan Najeriya sun gaji da halin da APC ta jefa su a ciki.

Kara karanta wannan

Rabiu Kwankwaso Ya Bayyana Abubuwa 2 da Zai ba Muhimmanci Idan Ya Samu Mulki

Sa'idu, Mamban NNPP mazaunin Hotoro a Kano, yace buɗe Ofishin Kamfe a Sharaɗa ya kaɗa hanjin da yawan 'yan siyasa ganin yadda jama'a suka fito.

A hirarsa da wakilin Legit.ng Hausa, Ɗan siyasan yace:

"Yadda mai gida (Kwankwaso) ya tara tulin mutane a Kano ya nuna cewa an gaji da yanayin da ake ciki, kowa ya san matsin da ake ciki musamman mu Magidanta. Mai gida ya fito ne ya magance matsalolin Najeriya."

Da yake tsokaci kan ko zasu iya kai labari a zaɓen 2023, Saidu Abdu, yace taron Kano ya kaɗa hanjin kowane ɗan siyasa kuma, "Da ikon Allah NNPP zata ba da mamaki kamar yadda Mai Gida ya faɗa.

A wani labarin kuma Shugabannin APC 16 Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar PDP a Jihar Sakkwato Gabanin 2023

Yayin da 'ya'yan jam'iyyar APC ke murnar dawowar Bola Tinubu, jam'iyyar ta yi rashin wasu shugabanninta na matakin gunduma a Sakkwato.

Kara karanta wannan

2023: Ana Shirin Bude Kamfe Yau, Atiku Ya Dauki Matakin Karshe Kan Rikicinsa da Gwamna Wike

Wasu shugabannin APC a gundumomi biyu dake karamar hukumar Sabon Birni sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP mai mulkin jihar ranar Jumu'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel