'Yan Daba Sun Kai Farmaki Kan Hadimin Gwamna Ganduje a Kano

'Yan Daba Sun Kai Farmaki Kan Hadimin Gwamna Ganduje a Kano

  • An samu wasu tsageru a jihar Kano da suka farmaki hadimin gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar
  • An zargi 'yan Kwankwasiyya da kai farmaki kan hadimin na Ganduje, Abubakar Balarabe Kofar Na'isa
  • Ana yawan samun tashin hankali tsakanin 'yan siyasa a Najeriya, musamman inda ra'ayi ya saba

Jihar Kano - Hadimin gwamna Ganduje na jihar Kano, Abubakar Balarabe Kofar Na'isa ya sha da 'kyar a hannun wasu 'yan daban da ake zargin 'yan Kwankwasiyya ne a jihar Kano.

Ana kuma zargin cewa, 'yan daban sun kwace wayar hadimin na gwamna Ganduje, Daily Trust ta ruwaito.

Balarabe ya bayyana cewa, an daba masa wuka a lokacin kana an farmaki wasu mutane da dama a Kofar Danagundi a jiya Lahadi 9 ga watan Oktoba da yamma.

Kara karanta wannan

Kano: Gini Mai Hawa Ɗaya Ya Rufta Wa Yara 3 Yan Gida Daya, Biyu Cikinsu Sun Mutu

An farmaki hadimin Ganduje a Kano
'Yan Daba Sun Kai Hari Kan Hadimin Gwamna Ganduje a Kano | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

Balarabe ya yada a shafinsa na Facebook cewa, 'yan ta'addan sun ci zarafin jama'a tare da aikata barnar da suka ga dama.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daily News 24 ta yada wani dan karamin hoton sako da Kofar Naisa ya fitar mai dauke da rubutun cewa:

"Yau na gamu da 'yan Kwankwasiyya a kofar Dan Agundi sun soka mun wuka sun kwacemun wayata wadda layin MTN dina yake a ciki.
"Amma cikin nufin ubangiji wukar da suka sokeni da ita bata kamani ba, amma sun tafi da wayar.
"Allah ya cigaba da kare ya kare mutuncinmu da rayuwarmu saboda alfarmar Annabi Muhammadu SAW."

Sai dai, ya bayyana cewa, bai samu mummunan rauni ba, amma dai tabbas sun yi awon gaba da wayarsa.

Duk da cewa an zargi matasan Kwankwasiyya da aikata wannan barna, har yanzu kungiyar bata yi martani a kai ba.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Ya Shiga Rudani, Ya Fadi Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu da Yake Son Zaben Daya a 2023

APC Ta Kaddamar da Tawagar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na Mata

A wani labarin, an kaddamar da sashen mata na tawagar kamfen din Tinubu na jam'iyyar APC gabanin zaben 2023 mai zuwa nan kusa.

A halin yanzu ne ake gudanar da kaddamarwar a Banquet Hall dake fadar shugaban kasa a Abuja, uma manyan jiga-jigan APC ne suka samu halarta, ciki har da shugaba Buhari.

Shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ma ya samu halarta, inji rahoton jaridar The Nation.

Asali: Legit.ng

Online view pixel