Tinubu Ya Yi Wa Wike Tayin Kujerar Sanata? Gwamnan Na Rivers Ya Fayyace Gaskiya

Tinubu Ya Yi Wa Wike Tayin Kujerar Sanata? Gwamnan Na Rivers Ya Fayyace Gaskiya

  • Gwamna Nyesom Wike ya nesanta kansa daga wani rahoto a kafafen watsa labarai na cewa ya ce dan takarar shugaban kasa na APC ya masa tayin tikitin takarar sanata
  • Gwamnan na Jihar Rivers, ta bakin hadiminsa na kafar watsa labarai, ya ce rahotonnin da suka yi ikirarin ya fadi hakan 'ba su da tushe'
  • Hadimin Wike, Ebiri' ya wallafa rubutaccen hirar da gwamnan ya yi da yan jarida kuma ya yi magana kan fom din takarar sanata

Rivers - Gwamna Nyesom Wike ya karyata rahotannin da ke cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu ya masa tayin tikitin takarar sanata ya sauya sheka bayan gwamnan na Jihar Rivers ya sha kaye a zaben cikin gida na shugaban kasa na PDP, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan Tona Asirin Wasu Jiga-Jigan PDP, Gwamna Wike Ya Yi Sabuwar Tafiya

Rahotannin sun yi ikirarin cewa Wike ya yi wannan jawabin ne yayin hirar da ya yi da manema labarai a ranar Juma'a amma hadimin gwamnan Kelvin Ebiri ya ce labaran 'ba su da tushe'.

Wike da Tinubu
Tinubu Ya Yi Wa Wike Tayin Kujerar Sanata? Gwamnan Na Rivers Ya Fayyace Gaskiya. Hoto: @OfficialBAT.
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Muna son mu bayyana cewa wannan labarin karya ne, ba shi da tushe, duba da cewa gwamnan na Jihar Rivers bai ambaci sunan dan takarar shugaban kasa na APC ko ya ce ya masa tayin tikitin sanata ba."

Ebiri ya kuma wallafa hirar da aka yi da gwamnan a rubuce inda gwamnan ya yi magana kan fom din takarar sanata kamar haka:

"Da farko, haka za ka gane wadanda suka shirya yin zabe. Wasu sun karba fom din takarar shugaban kasa sannan wasu sun karbi fom din takarar sanata. Za ka san cewa wadannan mutanen ba da gaske takarar za su yi ba.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Magana Bayan Fallasar Wike, Ya Bayyana Yadda PDP Za Ta Ci Zabe A 2023

"Ban taba karbar fom din takarar sanata ba. Bayan faruwar abin, mutane sun ce zo ka yi takarar sanata, na ce a'a. Ba zan yi haka ba. Na riga na yi alkawari cewa a mika kujerar sanata zuwa wannan yankin (Etche) domin ba su taba yin mulki ba. Ba dole sai na yi mulki ba."

Ya kara da cewa:

"A zamanin nan na rabuwar kai a siyasa, akwai yiwuwar sauya gaskiya sosai. Don haka muke kira ga yan jarida cewa aikinsu na farko shine fadin gaskiya.
"A wannan mai muhimmanci a kasarmu, muna son mu sanar da yan jarida su gane gaskiya shine ginshikin aikin jarida. Ana shawartar yan siyasa su rika fayyace gaskiya kuma su rika bayyana dukkan bayanan gaskiyan a rahotonsu. Don haka, muna kira ga al'umma su yi watsi da wannan rahoton na karya, mara tushe da madafa."

Masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi martani kan sanarwar na Wike

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa A 2023: Wasu Manyan Gwamnonin Arewa 3 Na Shirin Marawa Peter Obi Baya

Benedict Jackreece a Facebook ya ce:

"Idan Gwamna Wike na son tikitin takarar sanata da ya samu a jam'iyyar PDP ba tare da wahala ba."

Paulinus ya ce:

"Amma Wike ya furta hakan da bakinsa yayin hirar. Na saurari hirar kai tsaye."

Osita Edekobi ya ce:

"Idan ka fada magana ba ka saba wa. Ina son yadda ka ke magana. Ka cigaba da hakan gwamna na."

Suzor Louis ya ce:

"Ta yaya Tinubu zai ba wa Wike abin da zai iya samu cikin sauki kuma zai iya samu bayan ya sauka daga ofis a matsayin gwamna??
"Ina ganin giya ta yi yawa a tsarin Najeriya kuma wasu za su sha su rika magana duk yadda suke so ba tare da tunani ba."

Tikitin Musulmi Da Musulmi: Jerin Mukaman Da Kiristocin Najeriya Za Su Iya Samu A Gwamnatin Tinubu

A wani rahoton, bayan sukar da aka rika yi kan tikitin musulmi da musulmi da jam'iyyar APC ta yi, Kungiyar matasa kirista na 'Christian Youths Movement for Tinubu/Shettima' ta bayyana cewa akwai mukamai kiristoci za su iya samu idan Tinubu ya ci zaben 2023.

Kara karanta wannan

Wike Ya Fallasa Ayu, Ya Bayyana Babban Mukamin da Yake So Idan Atiku Ya Ci Zabe

Idan za a iya tunawa zaben tsohon gwamnan na Jihar Borno, Kashim Shettim a matsayin abokin takarar Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023 ya janyo cece-kuce a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel