Shugaban Kasa A 2023: Wasu Manyan Gwamnonin Arewa 3 Na Shirin Marawa Peter Obi Baya

Shugaban Kasa A 2023: Wasu Manyan Gwamnonin Arewa 3 Na Shirin Marawa Peter Obi Baya

  • Wani fitaccen mai rajin kare hakkin dan Adam a Najeriya, Kayode Ajulo, ya shawarci Peter Obi da ya kulla alaka a arewa gabannin babban zaben 2023
  • Ajulo ya yi kira ga tsohon gwamnan na Anambra da ya watsa kamfen dinsa har wajen kudancin kasar
  • Dan fafutukan ya bayyana cewa ya san wasu gwamnonin arewa 3 da ke shirin marawa Obi baya

AbujaGabannin babban zaben shugaban kasa na 2023, an rahoto cewa wasu manyan gwamnonin arewa uku sun nuna ra’ayinsu na son marawa kudirin Peter Obi baya.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa, Kayode Ajulo, wani mai rajin kare hakkin dan adam ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 23 ga watan Satumba, lokacin da ya zanta da manema labarai a Abuja.

Peter Obi
Shugaban Kasa A 2023: Wasu Manyan Gwamnonin Arewa 3 Na Shirin Marawa Peter Obi Baya Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Sai dai kuma, Ajulo bai ambaci sunayen wadannan gwamnoni da yace suna shirin marawa takarar shugabancin tsohon gwamnan na Anambra baya ba.

Kara karanta wannan

Borno: Matar Aure Ta Mutu Bayan Haihuwar Yan Uku A Sansanin Yan Gudun Hijira, Mijin Ya Bita Bayan 40

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ina sane da gwamnoni uku daga arewa wadanda suka nuna alamun mara masa baya.”

Duk da haka, mai fafutukar ya shawarci Obi da ya yi tuntuba har wajen kudancin kasar sannan ya yi amfani da kamfen dinsa wajen kulla gagarumin alaka a fadin Najeriya, ciki harda yankin arewacin kasar.

Ya yi hasashen cewa idan tsohon gwamnan na Anambra yayi fiye da abun da magoya bayansa ke yi a soshiyal midiya, labarin zai sauya zuwa mai dadi, rahoton Daily Nigerian.

Ya ce:

“Har yanzu zan ce Peter Obi bai shirya zama shugaban kasa ba, saboda bai shirya ketawa kogin Neja da ma Kogin Owena ba.
“Tallata kansa ga mutanen yankin arewacin kasar na iya sauya batun.”

'Yan Najeriya Sun Kai Wuya, Zasu Ba Wasu 'Yan Takara Mamaki A 2023, Gwamna

A wani labarin, gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya sun gaji da gwamnati a dukkan matakai, yana mai gargadin cewa masu zabe zasu ba yan siyasa da jam’iyyun siyasa mamaki a babban zaben 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan Lantarki Sun Yi Barazanar Kashe Wutan Najeriya Gaba Daya

Da yake zantawa da manema labarai a Benin, babban birnin jihar Edo, a ranar Talata, Obaseki ya ce yakamata yan siyasa su yi tsammanin abun mamaki daga masu zabe saboda rashin shugabanci mai kyau da kuma iya aiki, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel