Dan Takarar Shugaban Kasa, Al-Mustapha Ya Yi Ganawar Sirri da Gwamnan PDP Wike

Dan Takarar Shugaban Kasa, Al-Mustapha Ya Yi Ganawar Sirri da Gwamnan PDP Wike

  • Gwamnan PDP Wike na jihar Ribas ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa a karkashin jam'iyyar Action Allience (AA)
  • Hamza Al-Mustapha ya dira gidan gwamna Wike, inda suka yi ganawar da ba a san me suka tattauna ba
  • Ana takun-saka tsakanin gwamnan Wike da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar

Jihar Ribas - Gwamnan Nyesom Wike na jihar Ribas ya yi wata ganawar sirri da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AA, Hamza Al-Mustapha a gidansa dake Fatakwal a daren ranar Litinin 12 ga watan Satumba.

Manjo Al-Mustapha (mai ritaya), wanda shi ne babban dogarin marigayi tsohon shugaban kasa, Sani Abacha ya kai wata ziyara ce a jihar ta Ribas.

Gwamnan PDP ya mance Atiku, ya gana da dan takarar AA
Dan Takarar Shugaban Kasa, Al-Mustapha Ya Yi Ganawar Sirri da Gwamnan PDP Wike | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ziyarar ta Manjo na zuwa ne sama da mako guda bayan da masu neman kujerun gwamna 17 na jam’iyyar PDP a zaben 2023 suka zauna da Wike a Fatakwal.

Kara karanta wannan

Hotuna sun ba da mamaki yayin da Sarkin Musulmi ya gana da wani gwamnan Kudu

Meye dalilin ganawar Wike da Al-Mustapha?

Ya zuwa yanzu dai ba a san dalilin wannan ganawa, kuma ba wannan karon farko da gwamnan ya karbi bakuncin wasu 'yan takara ba na jam'iyyarsa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya daga gidan gwamnan Ribas ta shaidawa jaridar Punch cewa, gwamna Wike ko Al-mustapha babu wanda ya yiwa manema labarai bayanin me ya faru.

Sai dai, masu abin cewa na ganin ganawar na da alaka da neman goyon baya a zaben 2023 mai zuwa.

Haka nan, jaridar Daily Trust ta naqalto Al-Mustapha na cewa, ya kai ziyarar neman goyon baya ne ga gwamnan na PDP.

Tun bayan kammala zaben fidda gwanin shugaban kasa na PDP da kuma zabo gwamna Okowa a matsayin mataimakin Atiku, Wike ya karbi 'yan takara mabambanta a gidansa.

Akwai takun-saka tsakanin dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar da kuma shi wannan gwamna na PDP.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: PDP ta fadi matsayar ta kan ko Ayu zai ci gaba da kasancewa shugabanta

Jam’iyyar PDP Ta Karbe Ofisoshin Yakin Neman Zaben Buhari Na Katsina

A wani labarin, jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa, reshenta a jihar Katsina ya karbe ofisoshin yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar.

Shugaban jam'iyyar ne na kasa, Iyorchia Ayu ya bayyana hakan ga manema labarai a jihar, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Ayu ya samu wakilicin hadiminsa a fannin yada labarai, Yusuf A. Dingyadi a jihar Katsina, inda yace tuni jijiyoyin PDP suka mamaye sassa daban-daban na mahaifar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel