Jam’iyyar PDP Ta Karbe Ofisoshin Yakin Neman Zaben Buhari Na Katsina

Jam’iyyar PDP Ta Karbe Ofisoshin Yakin Neman Zaben Buhari Na Katsina

  • Da alamu jijiyoyin jam'iyyar PDP sun kara karfi a jihar Katsina yayin da ta bayyana kwaec ofishin kamfen din Buhari
  • Ana ci gaba da shirin zaben 2023, jam'iyyun siyasa na ci gaba da tallata 'yan takararsu gabanin zaben
  • Jam'iyyar PDP ta ce mafita ga 'yan Katsina shi ne su zabi jam'iyyar PDP a zabe mai zuwa saboda wasu dalilai

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Katsina - Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa, reshenta a jihar Katsina ya karbe ofisoshin yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar.

Shugaban jam'iyyar ne na kasa, Iyorchia Ayu ya bayyana hakan ga manema labarai a jihar, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Ayu ya samu wakilicin hadiminsa a fannin yada labarai, Yusuf A. Dingyadi a jihar Katsina, inda yace tuni jijiyoyin PDP suka mamaye sassa daban-daban na mahaifar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan Sanda Sun Damke Jiga-jigan PDP 2 Kan Zargin Zugawa Abacha Karya

Ya kuma bayyana cewa, jam'iyyar PDP ta yi matukar gazawa a jihar Katsina, lamarin da kara dagula rashin tsaro, talauci, rashin hadin kai da tabarbarewar tatalin arziki a jihar.

PDP ta karbe ofishin kamfen din Buhari a Katsina
Jam’iyyar PDP Ta Karbe Ofisoshin Yakin Neman Zaben Buhari Na Katsina | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za mu karbe ko ina, tunda APC ta gaza, inji Dingyadi

Ya jaddada aniyar PDP na ci gaba da karbe bangarori da yawa a Katsina, inda ya shaidawa jama'a cewa, mafita garesu daga halin da suke ciki shine zaben PDP a zaben 2023, rahoton Independent.

Da yake magana game da rikicin cikin gida da PDP ke fuskanta, Yusuf A. Dingyadi ya ce wannan ba sabon abu bane a siyasa, kuma jam'iyyar na yin ruwa da tsaki don warware matsalolinta.

Ya ce:

"Tuni mun riga mun warware dukkan matsalolin da suka shafi jam'iyya. Kwamitin amintattu (BoT) sun yi kuri'ar nuna kwarin gwiwa, majalisar zartaswa (NEC) da kuma kwamitin ayyuka duk sun nuna goyon baya ga shugaban jam'iyya na kasa tare da gyare-gyare da ayyuka masu kyau da ya fara."

Kara karanta wannan

Yanzun nan: PDP ta fadi matsayar ta kan ko Ayu zai ci gaba da kasancewa shugabanta

Gwamna Makinde Ya Maye Gurbin Tambuwal a Kujerar Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP

A wani labarin, jim kadan bayan da gwamnan jihar Sokoto Tambuwal ya sauka daga mukamin shugaban gwamnonin PDP, an sanar da gwamna Seyi Makinde a matsayin wanda ya maye gurbinsa.

Gwamnan Oyo ya zama sabon shugaban gwamnonin PDP ne a yau Alhamis 8 ga watan Satumba a taron majalisar zartaswar PDP dake gudana a Abuja.

An bayyana Makinde a matsayin sabon shugaban kungiyar ne mintuna kadan bayan da Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana yin murabus, rahoton 21st Century Chronicle.

Asali: Legit.ng

Online view pixel