Zaben Kwankwaso da Obi Zai Kara Wa Tinubu da Atiku Karfi Ne a 2023, Makarfi

Zaben Kwankwaso da Obi Zai Kara Wa Tinubu da Atiku Karfi Ne a 2023, Makarfi

  • Ahmed Makarfi, tsohon gwamnan Kaduna ya ce Kwankwaso da Obi ba zasu iya tabuka komai ba, sai taimakon APC ko PDP a 2023
  • Tsohon gwamnan ya yi kira ga jam'iyyun adawa su haɗa karfi su mara wa jam'iyyar PDP baya domin kawar da APC
  • Rabiu Kwankwaso na neman kujerar shugaban kasa a inuwar NNPP yayin da Peter Obi, ke nema a Labour Party

Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Maƙarfi, ya ce zaɓen Peter Obi na LP da Rabiu Kwankwaso na jam'iyyar NNPP, ɓata kuri'a ne domin zasu kara kafafa APC da PDP ne kawai.

The Cable ta rahoto Makarfi na cewa kamata ya yi Obi da Kwankwaso su koma jam'iyyar PDP domin taimaka wa jam'iyyar a kokarinta na ganin bayan APC a zaɓen shugaban ƙasan 2023.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: An Bukaci Gwamnan Wike Ya Yi Watsi da Atiku, Ya Koma Bayan Wannan Ɗan Takaran a 2023

Ahmed Makarfi.
Zaben Kwankwaso da Obi Zai Kara Wa Tinubu da Atiku Karfi Ne a 2023, Makarfi Hoto: thecableng.com
Asali: UGC

Da yake jawabi a shirin Sunrise Daily na Channels tv, ranar Talata, Maƙarfi yace ya kamata matasan Najeriya su kula kar su yi kuskuren yanke hukunci cikin fushi da ɓacin rai.

"Fafatawa zata yi zafi ne tsakanin APC da PDP, ya kamata mutane su sani, na san mutane suna cikin fushi da bacin rai amma zaɓi guda biyu ne ko dai ka zabi PDP ko APC."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Idan ka zaɓi wata jam'iyya daban, ka kara karfin ɗaya daga cikin waɗan nan jam'iyyun ne guda biyu, ya danganta da inda ka kaɗa kuri'ar. Gare ku matasa, idan kuna cikin fushi zaku iya ɗaukar mataki da zai ƙara munana yanayin da kuke ciki."
"Idan kana cikin bacin rai da fushi, ka nemi shawarin mutanen da zasu nema maka mafita. Amma idan ka ɗauki wani zaɓi da ba zai canza komai ba, meye amfanin fushin da ɓacin ran?"

Kara karanta wannan

2023: An Sanya Lokacin Sauya Shekar Shekarau Zuwa PDP, Atiku Zai Fara Zawarcin Wasu Yan Siyasan Kano

- Inji Maƙarfi.

Ya kamata sauran jam'iyyu su haɗa kai da PDP - Maƙarfi

Tsohon gwamnan ya yi kira ga sauran jam'iyyun adawa su haɗa karfi da jam'iyyar PDP domin kawo karshen mulkin APC a Najeriya.

"Ina kira ga jam'iyyun adawa su dunkule wuri ɗaya, musamman Peter Obi, na san yana ganin girman ɗan takarar PDP, yana girmama da yawan mu. PDP tamkar gidansa ne shi da magoya bayansa."
"Haka zalika Kwankwaso, tare da shi muka fara PDP, ya kamata mu koma gida mu yi abinda ya dace saboda ƙasar mu."

A wani labarin kuma Gwamna Wike dake takun saƙa da Atiku ya ce wani abu na gab da faruwa a jam'iyyar PDP

Gwamnan Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce ba abun da ya faru a jam'iyyar PDP amma nan ba da jimawa ba wani abu zai faru.

Wike wanda ke takun saƙa da Atiku, ɗan takarar shugaban kasa a PDP ya ce ba abinda zai razana shi wajen yin abinda ya dace.

Kara karanta wannan

2023: Daga Karshe, Shekarau Ya Yanke Jam'iyyar Da Zai Koma Bayan Ganawa da Atiku da Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel