2023: An Kammala Duk Wasu Shirye-Shiryen Sauya Shekar Shekarau Zuwa PDP Yau

2023: An Kammala Duk Wasu Shirye-Shiryen Sauya Shekar Shekarau Zuwa PDP Yau

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, zai koma jam'iyyar PDP a hukumance yau Litinin
  • Wata majiya ta ce manyan kusoshin PDP sun sa labule da Sanatan jiya Lahadi domin tsara komai game da lamarin
  • Atiku da wasu masu faɗa aji na PDP yanzu haka suna Kano kuma ana sa ran zasu shafe kwanaki a jihar

Kano - Malam Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano na tsawon zango biyu, zai sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a hukumance ranar Litinin wato yau.

The Cable ta ruwaito cewa Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban kasa a PDP da wasu jiga-jigan jam'iyyar suna birnin Kano domin karɓan Sanatan zuwa jam'iyyar.

Wani jigon PDP wanda ya nemi a ɓoye bayanansa, ya ce Alhaji Atiku zai zauna a Kano tsawon kwanaki uku domin zawarcin wasu mambobin jam'iyyun adawa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku Da Wasu Jiga-Jigan PDP Sun Dira Birnin Kano Kan Sauya Shekar Shekarau

Malam Ibrahim Shekarau.
2023: An Kammala Duk Wasu Shirye-Shiryen Sauya Shekar Shekarau Zuwa PDP Yau Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Ya bayyana cewa ƙusoshin jam'iyyar PDP sun gana da Malam Shekarau ranar Lahadi domin tabbatar wa da tsara ficewarsa daga jam'iyyar NNPP mai kayan marmari.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majiyar ta ce:

"A yanzu da nike magana da ku, mun zauna da Shekarau a gidansa kuma muna kan kokarin tsara sauya sheƙarsa da sauran mutanen sa zuwa PDP. Mun kammala duk shirye-shirye."
"Shugabannin mu na jam'iyya sun shirya tsaf don tabbatar da nasarar ziyarar ɗan takarar mu na kujerar shugaban kasa, Atiku Abubakar, da shugaban PDP na ƙasa, Dr Iyorchia Ayu."
"Atiku zai kwana uku a Kano domin zawarcin mambobin adawa zuwa PDP, ina da ƙwarin guiwar mu zamu lashe zaɓen 2023. Atiku zai gana da kungiyoyin Malamai, matasa da sauran su domin jawo hankalin su zaɓe shi a 2023."

Meyasa Shekarau ya bar PDP a baya?

Kara karanta wannan

2023: Daga Karshe, Shekarau Ya Yanke Jam'iyyar Da Zai Koma Bayan Ganawa da Atiku da Tinubu

Har zuwa 2018, Shekarau ya kasance mamban jam'iyyar PDP, kafin daga bisani ya fice saboda rikicin da ya barke a jam'iyyar reshen Kano. Ya koma APC a 2019, inda ya nemi Sanata kuma ya yi nasara.

Watanni kaɗan da suka gabata, ya sauya sheka zuwa NNPP bayan samun saɓani da gwamna mai ci, Dakta Abdullahi Ganduje, kan shugabancin jam'iyya, jaridar Punch ta ruwaito.

A makon da ya gabata, Shekarau ya sanar da cewa ya raba gari da NNPP, inda ya zargi Rabiu Musa Kwankwaso da cin amanar yarjejeniyar da suka yi gabanin shigarsa jam'iyyar.

A wani labarin kuma Sabuwar Matsala a PDP, Ɗan Takarar Gwamna Ya Fice, Ya Koma Bayan Wanda Yake So Ya Gaji Buhari a 2023

Tsohon ɗan takarar gwamnan Anambra, Valentine Ozigbo, ya tabbatar da ficewarsa daga PDP a wani taro jiya.

Ozigbo, ya ce ba zai iya raba jam'iyya tsakaninsa da Peter Obi ba, wanda ya kira ɗan uwansa, uban gidansa kuma jagora.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Shirya Zuwa Kano Domin Dauke Shekarau Daga Jam’iyyar NNPP zuwa PDP

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel