Daga Karshe, Malam Ibrahim Shekarau Ya Yanke Jam'iyyar da Zai Koma Bayan Fita NNPP

Daga Karshe, Malam Ibrahim Shekarau Ya Yanke Jam'iyyar da Zai Koma Bayan Fita NNPP

  • Tsohon gwamnan Kano ya amince ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP kuma Atiku da kansa zai karɓe shi yau Lahadi
  • Shugaban PDP, Shehu Wada Sagagi, ya ce shirye-shirye sun yi nisa na zuwan Atiku da kuma dawowar Malam Ibrahim Shekarau
  • Sanata Shekarau mai wakiltar Kano ta tsakiya ya raba gari da NNPP ne bayan gaza baiwa mutanensa tikitin takara a 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Alhaji Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa zai ziyarci jihar Kano ranar Lahadi (yau) domin karɓan Sanatan Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau zuwa jam'iyyar PDP.

Daily Trust ta ruwaito cewa Sanata Shekarau ya fice daga PDP zuwa APC ne yayin da ake shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2019 da ya gabata.

Sanata Mallam Ibrahim Shekarau.
Daga Karshe, Malam Ibrahim Shekarau Ya Yanke Jam'iyyar da Zai Koma Bayan Fita NNPP Hoto: Abubakar Ibrahim Jega/facebook
Asali: Facebook

Karkashin inuwar jam'iyya mai mulki ne ya lashe zaɓen Sanatan Kano ta tsakiya. A halin yanzu, ya samu saɓani da gwamna Abdullahi Umar Ganduje, hakan ta sa ya koma NNPP mai kayan marmari.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Shirya Zuwa Kano Domin Dauke Shekarau Daga Jam’iyyar NNPP zuwa PDP

Sai dai watanni kalilan bayan sauya shekar Shekarau zuwa sabuwar jam'iyyar, alaƙarsa ta yi tsami da jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Kwankwaso bayan mutanen Sanatan ba su samu tikitin takara ba kamar yadda aka musu alƙawari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatan ya gana da ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, inda ya masa tayin muƙamai masu gwabi kuma daga bisani ya gana da Bola Tinubu, mai neman gaje Buhari a APC.

Tsohon gwamanan na kan hanyar komawa jam'iyyar PDP, domin wata majiya ta tabbbatar da cewa shirye-shirye sun kammalu wajen ganin Shekarau ya ƙara karfin tawagar Kanfen ɗin Atiku a Kano.

Shekarau ya amince ya dawo PDP - Sagagi

Da yake jawabi ga jaridar Dailytrust, shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Kano, Shehu Wada Sagagi, ya bayyana cewa Shekarau ya amince ya dawo jam'iyyar hammayya PDP.

Kara karanta wannan

Daga karshe: NNPP ta yi magana game da yiwuwar hadewar Kwankwaso da Tinubu a 2023

Ya ce:

"Mun gode Allah, daga karshe mun samu jagora a jihar Kano kuma na ji daɗin haka. Shekarau, kasancewarsa mai rike da babban ofishin siyasa, ya amince kuma muna masa maraba da dawo wa jam'iyyar mu PDP."
"Shirye-shirye sun yi nisa na karɓan baƙuncin Atiku Abubakar, wanda zai ziyarci Kano ranar Lahadi, muna fatan shi zai karɓi tuban Malam Shekarau. Mun yarda mu masa biyayya kuma nasara ta mu ce da ikon Allah."

A wani labarin kuma Ministar jin kai da walwala ta ce da ikon Allah Mijinta ne zai lashe zaɓen gwamnan Bauchi a 2023

Ministar harkokin jin kai da walwala, Hajiya Sadiya Farouq, ta ce idan Allah ya so mijinta ne gwamnan jihar Bauchi na gaba a 2023.

Hajiya Sadiya, Minista mafi karancin shekaru a gwamnatin Buhari, ta ce Sadique Abubakar mutum ne da kowa zai so ya zama gwamna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel