Daga karshe Atiku Abubakar ya yi maganar ‘rigimarsa’ da Gwamna Wike a PDP

Daga karshe Atiku Abubakar ya yi maganar ‘rigimarsa’ da Gwamna Wike a PDP

  • Dazu aka ji Alhaji Atiku Abubakar yace babu wani rikici tsakaninsa da Gwamnan Ribas watau Nyesom Wike a jam’iyyar PDP
  • Kamar yadda Atiku Abubakar ya fada a wani jawabi, maganar rikicin gidan PDP da ake yi, sharrin jam’iyyar APC mai mulki ne
  • Wazirin Adamawa yace kan Nyesom Wike da sauran Gwamnonin PDP a hade yake wajen ganin an yi waje da gwamnatin APC

London - Atiku Abubakar mai neman zama shugaban Najeriya a karkashin PDP ya gargadi jagororin jam’iyyar hamayyar game da sakin bakinsu.

The Cable ta kawo rahoto a daren Juma’a, 26 ga watan Agusta 2022 cewa Atiku Abubakar ya bukaci manyan PDP su guji kalaman da za su raba kai.

Ganin yadda wasu ke sakin kalamai a game da abubuwan da ke faruwa a jam’iyya, ga kuma zabe ya karaso, Atiku ya fadawa abokan aikinsa su yi hattara.

Kara karanta wannan

Sai an gyara: Shugaba a PDP Ya Yarda Akwai Zalunci a Jam’iyya a Rabon Kujeru

A wani jawabi da ya fito daga bakin Paul Ibe, ‘dan takaran shugaban kasar ya nuna cewa babu rabuwar kai tsakaninsa da ‘yan bangaren Nyesom Wike.

Paul Ibe wanda shi ne Kakakin Atiku Abubakar yace al’umma suna sa ran PDP ta karbe mulki.

Jawabin da Paul Ibe ya fitar

“Ya zama dole ayi kira ga duka ‘ya ‘ya da jagororin jam’iyya da duk masu alaka da ‘dan takaran PDP, Atiku Abubakar, su kauracewa yin kalaman da za su iya taba kimar PDP a matsayin jam’iyya mai hadin-kai.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Atiku Abubakar
Atiku tare da su Wike a Landan Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC
“Wannan kira ya zama ole domin jawo hankalin wasu jagorori da ‘ya ‘yan jam’iyya a game da dabarar APC na kokarin nunawa mutane cewa akwai baraka a PDP domin su jawo a manta da gazawarsu.”

Sharrin APC ne wannan - Atiku

Jawabin yake cewa APC ta kirkiri rade-radin rikicin cikin gida a PDP saboda hango faduwa zabe. A cewar Atiku, APC ba ta da abin tallatawa a 2023.

Kara karanta wannan

Hantar Atiku da PDP Ta Kada Bayan Samun Bayanin Zaman Tinubu da Wike a Landan

“A yau ‘Yan Najeriya suna duban PDP domin ta hambarar da jam’iyya mai mulki. Wannan kallon da mutane ke yi mana, ya jawo APC ta ke fushi a kan shan kasan da za tayi a babban zaben mai zuwa.”
“Sun san babu abin da za su yi kamfe da shi daga mulkin da suka yi. A kan wannan nake rokon uk mai son ‘dan takaran PDP da nasara, ya guji biyewa dabarun APC da zai iya nuna akwai baraka a PDP.”

A karshen jawabin, Punch ta rahoto Atiku yana cewa Nyesom Wike da sauran Gwamnonin PDP suna aiki ne domin ganin PDP tayi nasara a badi.

Tinubu zai fadi a Legas

An ji labari cewa Dino Melaye yana nan ya dage Bola Tinubu na APC da kuma sauran ‘Yan takaran Shugaban kasa a zabe mai zuwa ba za su kai labari ba.

Ganin yadda zaben Osun ya kasance, Sanata Dino Melaye yana ganin jam’iyyar PDP za ta shiga har Legas, ta koyawa Asiwaju Bola Tinubu darasi a siyasa.

Kara karanta wannan

Taron NBA: Abin da Atiku, Obi suka fada, yayin da aka nemi Kwankwaso aka rasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel