Tawagar Gwamna Wike da Ta Atiku Sun Shigawa Ganawar Sirri Don Neman Sulhu
- Rahoton da muke samu daga jihar Ribas ya bayyana cewa, gwamnan jihar Adamawa ya jagoranci tawagar tattaunawa da 'yan tsagin Wike
- Ana zaman doya da manja tsakaninAtiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a PDP da gwamnan jihar Ribas Wike
- Gwamna Wike ya bayyana matsayarsa cewa, ba zai yiwa kowace jam'iyya dariya ba wajen kare jiharsa daga matsaloli
Fatakwal, jihar Ribas - Daga karshe dai sashen gwamnan Ribas Nyesom Wike da na dan takarar shugaban kasan jam’iyyar PDP mai adawa, Atiku Abubakar sun gana a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas domin dinke baraka.
A cewar rahoton jaridar The Nation, ganawar ta samu halartar gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri a matsayin jagoran tawagar Atiku da, inda suka dira fadar gwamna Wike a madadin Atiku.
Tun bayan kammala zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP na dan takarar shugaban kasa Wike da Atiku ke zaman doya da manja saboda wasu mabambantan ra'ayoyi da ke tsakani.
Atiku ya kara tunzura Wike tun bayan da ya zabi gwamnan Delta, Okowa a matsayin abokin gami a takararsa, lamarin da ya fusata gwamnan da ma 'yan a mutunsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An kallama tattaunawa
Wani bidiyo da wakilinmu ya gano daga jaridar Vanguard ya nuna lokacin da wadanda suka halarci zaman ke fitowa.
Fintiri ya shaidawa manema labarai cewa, nan ba da jimawa za a samu daidaito tsakanin Atiku da Wike, kana jam'iyya ta zauna lafiya.
Sai dai, wata majiyar cikin taron ta shaidawa Vanguard cewa, har yanzu dai ba a samu wata matsaya ba, kuma akwai dambarwar da ke tsakani duk da wannan zama.
Yadda Gwamnatin Wike Ta Garmake Otal da Mashayar Jigon Siyasar Dan Takarar PDP Atiku
A wani labarin kuma, wani rahoton jaridar Punch ya bayyana cewa, jami'an tsaro da sanyin safiyar yau Juma'a suka garkame otal da matasha, gidan mai mallakin wani jigon siyasar jam'iyyar PDP.
An garkame otal da mashayan ne da ke a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas saboda gudanar wani taro ba bisa ka'ida ba.
Hakazalika, an kame wasu mutane da ke da hannu da taron, ciki har da ma'aikatan da ke aiki a wurin.
Asali: Legit.ng