Bayan an kammala zaben APC, Fadar Shugaban kasa ta yi maganar ‘Dan takarar Buhari'

Bayan an kammala zaben APC, Fadar Shugaban kasa ta yi maganar ‘Dan takarar Buhari'

  • Fadar Shugaban kasa ta ce babu wasu boyayyun masu rike da madafan iko a gwamnatin Buhari
  • Garba Shehu ya fitar da jawabi yana cewa shugaba Muhammadu Buhari ba ya zarce huruminsa
  • Hadimin ya ce ‘dan takarar Mai girma shugaban kasa shi ne duk wanda Jam’iyya ta tsaida a 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Fadar shugaban kasar Najeriya ta fito ta yi watsi da zargin da ake yi na cewa akwai wasu boyayyun mutane da su ke juya madafan iko a Aso Villa.

Channels TV ta ce Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya fitar da jawabi, yana karyata wannan rade-radi bayan zaben APC.

Garba Shehu ya yi wa jawabinsa take da “President’s Laudatory Role in the APC Primary” domin bayanin rawar da Buhari ya taka a zaben ‘dan takaran APC.

Kara karanta wannan

2023: Watakila Bola Tinubu ya dauki Musulmi a ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa

“Gidajen yada labarai su na yawan kawo rahotanni – ana hasashen rawar da shugaban kasa ya taka wajen tsaida ‘dan takaran shugaban kasa
Ana batun ko shugaban kasa yana da ‘dan takara, ko ya yi kutun-kutun domin ya ba su tikiti, ko wanda aka zaba zabinsa ne, da sauransu.

Wanene 'dan takaran Buhari?

Hasashe irin wannan yana da saukin yi, amma gaskiya ta na da sauki. Shugaban kasa ya na da ‘dan takara; shi ne duk wanda aka tsaida.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban kasa
Shugaban kasa da manyan Gwamnati bayan zaben APC Hoto: GarShehu
Asali: Facebook

“Ya fada cewa ‘dan takararsa shi ne kowane APC ta tsaida a zaben gaskiya na fitar da gwani domin ya jagoranci jam’iyya a zaben 2023.”

Garba Shehu ya cigaba da cewa wasu mutanen su na tunanin idan mutum shugaba ne, shikenan zai mamaye komai, har ya kutsa kai a sakamakon zabe.

Kara karanta wannan

2023: A karon farko, Bola Tinubu ya tabo magana game da wanda zai zama Mataimakinsa

A cewarsa, Najeriya ta yi dace ganin babu ruwan Buhari da wannan kama-karya, ya ce shugaban kasar ba shugaban karfi da yaji ba ne a rigar farar hula.

Burin Muhammadu Buhari

An rahoto Shehu yana cewa manufar Buhari ita ce gudanar da zaben tsaida gwani na ke-ke-da-ke-ke da gaskiya ta yadda za a iya wa kowa adalci a jam’iyya.

Hadimin shugaban Najeriyan ya ce darajar Najeriya ta karu a idanun kowa a Duniya bayan APC ta fitar da ‘dan takara ba tare da an samu rigimar komai ba.

Peter Obi zai kai labari?

A zaben 2023, an ji labari zai yi wahala LP ta iya samun kuri’un Arewa, kuma zai yi wahala yin galaba a kan PDP da APC a Kudu domin su na da gwamnoni.

Takarar Peter Obi za ta fuskanci matsala saboda har gobe Jam’iyyarsa ta LP ba ta da Gwamna ko wasu gogaggun ‘yan siyasa duk da irin karbuwar da ya yi a yau.

Kara karanta wannan

EFCC za ta damke ‘Yan takara inji Mai neman tikitin APC da ya kashe N100m, ya samu kuri’a 0

Asali: Legit.ng

Online view pixel