Zaben fidda gwanin APC: Akpabio ya yi zazzafan martani game da janyewa daga tseren shugabancin kasa

Zaben fidda gwanin APC: Akpabio ya yi zazzafan martani game da janyewa daga tseren shugabancin kasa

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci yan takarar shugaban kasa na APC da su fitar da dan takarar maslaha
  • Sai dai kuma, Godswill Akpabio wanda ya kasance daya daga cikin yan takarar ya ce yana nan a kan bakarsa ta son zama shugaban kasa a 2023
  • Tsohon gwamnan na Akwa Ibom ya bukaci deleget da su yi watsi da rade-radin da ke yawo cewa ya janye daga tseren

Daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Godswill Akpabio, ya bayyana cewa ba zai janye daga tseren kujerar ba.

Hakan na zuwa ne yan awanni bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki sannan ya bukaci da su fito da dan takarar maslaha.

Kara karanta wannan

Ba zai taba goyon bayan Tinubu ba: Sule Lamido ya bayyana mutum 2 da Buhari yake so ya tsayar a 2023

Zaben fidda gwanin APC: Akpabio ya yi zazzafan martani game da janyewa daga tseren
Zaben fidda gwanin APC: Akpabio ya yi zazzafan martani game da janyewa daga tseren Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

A cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook, tsohon gwamnan na jihar Akwa Ibom, ya bayyana rade-radin cewa ya janye daga tseren a matsayin mugun karya.

Ya kuma bukaci deleget din jam’iyyar mai mulki da su yi watsi da jita-jitan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya rubuta a shafin nasa:

“Ya ku deleget din APC na kasa, dan Allah ku yi watsi da mugun karyan da ke yawo cewa ni, zabinku, na kujerar shugaban kasar Najeriya a 2023, na janye daga tseren. Ban janye daga tseren ba kuma na san kuna tare da kudirina. Ba zan janye ba saboda ina da goyon bayanku.
"Tare za mu yi nasara kuma ni ne zan zama dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyarmu, mu yi tattaki tare don cin zaben shugaban kasar. Ina cikin tsere tare da goyon bayanku don samun nasara. Ina godiya kuma Allah ya saka muku da alkhairi."

Kara karanta wannan

Hotuna: 'Yan a mutun Jonathan sun mamaye hedkwatar APC suna neman a ba shi tikiti

Ba zai taba goyon bayan Tinubu ba: Sule Lamido ya bayyana mutum 2 da Buhari yake so ya tsayar a 2023

A wani labarin kuma, babban jagoran jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Sule Lamido, ya ce yana hasashen juyin mulki a zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Lamido ya ce wannan juyin mulki ne zai kai ga samar da tikitin shugaban kasa na shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi.

Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 5 ga watan Yuni, yayin da yake zantawa da jaridar Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel