Hotuna: 'Yan a mutun Jonathan sun mamaye hedkwatar APC suna neman a ba shi tikiti

Hotuna: 'Yan a mutun Jonathan sun mamaye hedkwatar APC suna neman a ba shi tikiti

  • A yau ne masoyan tsohon shugaban kasa Jonathan suka mamaye hedkwatar jam'iyyar APC suna zanga-zanga
  • Sun bayyana cewa, suna bukatar jiga-jigan jam'iyyar APC su duba tare da ba tsohon shugaban kasar tikiti
  • Bidiyo da hotuna sun yadu, inda aka ga jama'ar dauke da allunan nuna goyon baya ga Goodluck Jonathan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Wasu 'yan a mutun tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a ranar Juma’a sun yiwa hedikwatar jam’iyyar APC kawanya, inda suka bukaci a dauke shi a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Har yanzu dai Jonathan bai bayyana aniyar tsayawa takarar shugaban kasa a hukumance ba, TheCable ta ruwaito.

Ba a ambaci sunan tsohon shugaban ba a cikin jerin wadanda jam’iyyar APC ta wanke domin fafatawa a zaben fidda gwanin shugaban kasa.

Hotunan masoya Jonathan a bakin sakateriyar APC
Hotuna: Yadda 'yan a mutun Jonathan suka mamaye hedkwatar APC suna neman a ba shi tikitin 2023 | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

A wani lokacin cikin watan Afrilu, bai ba da amsa karara ba kan kiran da aka yi masa na ya tsaya takarar shugaban kasa a lokacin da wasu magoya bayansa suka nemi hakan gidansa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: APC ta magantu kan batun takarar Jonathan a zaben fidda gwanin shugaban kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa wancan lokacin:

“Kuna kirana da in zo in bayyana aniyar takara a zabe mai zuwa. Ba zan iya gaya muku zan ayyana ba. Tsarin tafiyar na dai gudana. Ku dai jira kawai.”

Tsohon shugaban kasar ya kuma yi watsi da ikrarin wata kungiyar Arewa da ta saya masa fom din takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.

A yau ma wasu masoyansa sun yi mamaye hedkwatar APC domin nema masa tiki.

Kalli bidiyon mamayewar tasu:

2023: Kwamitin tantancewar APC ya kori 10 daga cikin 'yan takarar shugaban kasa

A wani labarin, wani rahoton da This Day ta fitar ya ce, kwamitin tantance 'yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya kori mutane 10 da za su fafata a zaben fidda gwani da za a yi a mako mai zuwa.

Shugaban kwamitin, John Oyegun ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ina zama shugaban kasa zan saki shugaban IPOB Nnamdi Kanu, dan takara

A cewar Mista Oyegun, 13 ne kawai cikin 23 da kwamitin ya tantance za su fafata a zaben na mako mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel