El-Rufai: A yafe mana, mun gagara kare jama’a, ban san abin da zan fadawa Allah a lahira ba

El-Rufai: A yafe mana, mun gagara kare jama’a, ban san abin da zan fadawa Allah a lahira ba

  • Gwamnan Jihar Kaduna ya koka game da yadda matsalar tsaro ya tabarbare a karkashin mulkinsu
  • Malam Nasir El-Rufai ya nemi wadanda ya ke mulka su yi masa afuwa domin ya gagara ba su kariya
  • Mai girma gwamnan ya roki al’umma ne a lokacin da ya je yi wa mutanen garin Giwa ta’aziyya

Kaduna - Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya roki mutanensa su yafe masu bayan hare-haren da aka rika kai masu a ‘yan kwanakin nan.

Wani rahoton BBC Hausa ya ce Mai girma Nasir El-Rufai ya yarda cewa shugabannin da suke kan karagar mulki sun yi wasa da rayuka da dukiyar mutane.

Gwamnan da tun a ranar Litinin ya ke cikin bakin ciki, ya shaida cewa rabon shi da ya yi barci tun a ranar Alhamis duk da ya na shan magungunan barci.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Mun san inda 'yan bindiga suke, abu daya ne ya hana mu farmaki maboyarsu

Rahoton da aka fitar a jiya ya ce Malam El-Rufai ya yi wannan jawabi sa’ilin da ya ziyarci karamar hukumar Giwa domin ya yi wa Bayin Allah ta’aziyya.

A karshe Gwamna ya je Giwa

Ziyarar gwamnan ta zo ne bayan an dauki mako guda ‘yan bindiga su na yin ta’adi a yankin Giwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai girma mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Sabuwa Balarabe da wasu mukaraban gwamnati su ka samu yi wa El-Rufai rakiya.

Gwamna El-Rufai
Malam Nasir El-Rufai Hoto: @govkaduna
Asali: Facebook

Za ayi bayani a filin kiyama

An ji gwamnan a ta’aziyya da jajen da yake yi wa mutanensa ya na cewa hakkin shugabancin al’umma nauyi ne da zai tsaida mutum a gaban Ubangiji.

El-Rufai ya ce wata rana zai tashi ya yi bayani a gaban Allah madaukakin Sarki. Gwamnan yake cewa za a nemi a ji irin kokarin da ya yi domin tsare jiharsa.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Albarkatun Ruwa Na Jihar Kano Ya Ajiye Aikinsa

Kamar yadda aka rahoto, El-Rufai ya ce yana tsoron haduwarsa da Ubangiji, a dalilin haka ne ya ga bukatar ya nemi gafara da afuwa saboda gazawarsa.

Mai girma El-Rufa'i yana ganin shugabanni irinsa ba su da uzuri a gaban Allah a lokacin da za a tare su a madakata a ranar kiyama domin ayi wa kowa hisabi.

Duk da jama’a su na da laifi, gwamnan ya ce nauyin ya fi rataya ne a kan masu mulki ganin yadda karamar matsala ta gagari gwamnati har tsawon shekaru uku.

Na gama taba El-Rufai

Da yake magana a shafin Twitter, Aliyu Kwarbai ya yi alkawari ba zai kara sukar El-Rufai ba. Wannan matashi ya yi suna wajen adawa ga gwamnatin APC.

“Daga yanzu, ba zan sake sukar Nasir El-Rufai ba. Ya yarda cewa jam’iyyarsu ta ba ‘Yan Najeriya kunya.
Allah ya cigaba da taimakawa shugabanninmu da kasarmu baki daya. Najeriya ce farko a gaba na.” - Aliyu Kwarbai

Kara karanta wannan

El-Rufai Ya Magantu Kan Harin Jirgin Kasan Kaduna: Na Gargadi Gwamnatin Tarayya Ta Dena Jigilar Fasinjoji Da Daddare

Asali: Legit.ng

Online view pixel