Yan takarar shugaban ƙasa uku na PDP sun gana da IBB kan batun wanda zai gaji Buhari a 2023

Yan takarar shugaban ƙasa uku na PDP sun gana da IBB kan batun wanda zai gaji Buhari a 2023

  • Bukola Saraki, Aminu Tambuwal da Bala Muhammed sun gana da IBB kan batun fitar da ɗan takara ta hanyar sulhu
  • Jiga-jigan PDP guda uku dake neman takarar shugaban ƙasa sun nemi Babangida ya taimaka musu da shawara kan 2023
  • Tsohon shugaban ƙasa ya nuna jin daɗinsa matuka game da kunshin da yan takarar suka je masa da shi

Niger - Yan takarar kujerar shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar PDP guda uku sun gana da tsohon shugaban ƙasa a mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya.

Dailytrust ta rahoto cewa yan takarar, gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto, gwamna Bala Muhammed na Bauchi da tsohon gwamnan Kwara, Bukola Saraki, sun tattauna da IBB ne kan yuwuwar yin sulhu.

Gwamnan Bauchi, Gwamnan Sokoto da Bukola Saraki.
Yan takarar shugaban ƙasa uku na PDP sun gana da IBB kan batun wanda zai gaji Buhari a 2023 Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Da yake jawabi a madadin sauran yan tawagar, Saraki ya ce sun ziyarci IBB ne domin neman shawarinsa da kuma sa su a hanyar fitar da ɗan takara ɗaya da kowa zai amince.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Kwamishina ya yi murabus daga muƙaminsa, ya sayi Fam ɗin takara a PDP

A kalamansa ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mun zo nan ne a wnai ɓangaren yawon neman shawari da muke yi a faɗin ƙasar nan, mu tattauna da shugabanni da masu faɗa a ji na jam'iyyar mu PDP."
"Mu, yan takara a PDP muka ga ya dace mu zo gaban tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja kan abun da muke shiri na martaba tsarin sulhu. Mun yi amanna cewa a irin haka, muna bukatar shawarinsa da haska mana."
"Muna kokarin samar da maslaha a matakin siyasa, muna haka ne don tabbatar da abun bai yi zafi ba. Ba zamu iya mu huɗu kacal ba, muna bukatar goyon bayan shugabannin mu da shawarwarin su."

Yace daga ƙarshe, ɗan takarar dake da goyon bayan yan Najeriya, shi jam'iyya zata ba tutar takara a zaɓen dake tafe.

Na ji daɗin kokarin da kuke yi - IBB

Kara karanta wannan

Yadda zan jagoranci jam'iyyar APC ta samu nasara a 2023. Sanata Adamu ya magantu

Da yake martani, Babangida ya bayyana cewa ya ji matuƙar daɗi da matakin fidda ɗan takara ta hanyar sulhu, wanda a cewarsa zai buɗe kofar zaman lafiya a Najeriya.

"Na ji daɗin gana wa da ku saboda ina son abin da naji kun faɗa. Yaƙinin ku kan dunƙulewar ƙasar nan shi ne babban abu mai muhimmanci. Duk abin da kuke magana a kai ya danganci gyara Najeriya."

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP ta samu gagarumin koma baya, Ɗan takarar gwamna ya yi murabus

Ɗan takarar gwamna a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar PDP a jihar Osun ya yi murabus daga kasancewarsa mamba.

Dakta Akin Ogunbiyi, jigo a PDP reshen Osun ya bayyana haka ne a wata wasika da ya aike wa shugaban jam'iyya na ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel