Rikicin PDP: Kwamishina ya yi murabus daga mukaminsa, ya siya Fam ɗin takarar gwamna a 2023

Rikicin PDP: Kwamishina ya yi murabus daga mukaminsa, ya siya Fam ɗin takarar gwamna a 2023

  • Kwamishinan muhalli da albarkatun karkashin ƙasa na Enugu ya yi murabus daga kan mukaminsa
  • Mista Edeoga, ya ce ya ɗauki wannan matakin ne domin maida hankali kan burinsa na zama gwamna a 2023
  • Ya gode wa Allah bisa taimakonsa lokacin da yake kan kujera, ya kuma gode wa gwamna da ma'aikan da ya yi aiki tare da su

Enugu - Kwamishinan muhalli da ma'adanan ƙasa na jihar Enugu, Mista Chijioke Edeoga, ya yi murabus daga majalisar zartarwan jihar.

Jaridar Punch ta gano ranar Laraba cewa, Kwamishinan, wanda tsohon shugaban kwamitin labarai na majalisar dokoki ne, ya aje muƙaminsa tun ranar Jumu'a.

Mista Edeoga, ya yi jawabin bankwana ga ma'aikatan ma'aikatar da ya bari ranar Laraba, kuma rahoto ya nuna cewa ya sayi Fam ɗin takarar gwamna ƙarƙashin PDP a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Yadda zan jagoranci jam'iyyar APC ta samu nasara a 2023. Sanata Adamu ya magantu

Kwamishinan Enugu ya yi murabus.
Rikicin PDP: Kwamishina ya yi murabus daga mukaminsa, ya siya Fam ɗin takarar gwamna a 2023 Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa Kwamishinan ne mutum ɗaya tilo da ya yi murabus domin neman kujera lamba ɗaya a Enugu kuma ana ganin yana da karfi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake jawabi a tsohuwar ma'aikatarsa, Edeoga, ya ce ya ɗauki wannan matakin ne a karan kansa domin samun damar mauda hankali kan burinsa a siyasa da kuma biyayya da Kundin zaɓe 2022.

Ya ce:

"Game da babban zaɓen 2023 kuma gaskiya na tattare da mu, mafi yawan al'umma na goyon bayan mu. Da yardar Allah nasara zata tabbata."

Ya kuma gode wa Allah bisa taimaka masa wajen tafiyar da harkokin ma'aikatar da ya jagoranta na tsawon lokaci, tun daga 2019 zuwa ranar da ya yi murabus.

Bayan haka ya gode wa shugabanni da ma'aikatan ma'aikatar bisa ɗumbin goyon baya da haɗin kan da suka ba shi yayin aiki tare da su.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta samu gagarumin koma baya, Ɗan takarar gwamna ya yi murabus

Edeoga, ya kuma ƙara gode wa gwamna Ugwuanyi na jihar Enugu, bisa tsamo shi ya yi aiki karkashin gwamnatinsa a matsayin kwamishina tun daga 2015 zuwa yau.

Shugaban matasan APC ya yi hatsari a Oyo

A wani labarin kuma Shugaban matasan APC da wani babban jigo sun yi hatsari, Allah ya musu rasuwa

Allah ya yi wa shugaban matasan APC rasuwa da wani mamba da suke tare sanadiyyar hatsarin Mota a jihar Oyo.

Rahoto ya nuna cewa mutanen biyu na cikin Mota a kan hanyarsu ta komawa gida wata Tirela ta dakon siminti ta niƙe su

Asali: Legit.ng

Online view pixel