2023: ‘Dan takarar Shugaban kasa ya gargadi PDP, ya fada mata abin da zai sa ta fadi zabe

2023: ‘Dan takarar Shugaban kasa ya gargadi PDP, ya fada mata abin da zai sa ta fadi zabe

  • Anyim Pius Anyim ya ziyarci jihar Filato a yunkurinsa na ganin ya zama ‘dan takarar PDP a 2023
  • Sanata Anyim Pius Anyim ya na cikin masu harin neman takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa
  • Tsohon shugaban majalisar dattawan ya ce ya kamata a dauko mutumin Kudu a 2023 idan da adalci

Pleatau - Anyim Pius Anyim wanda yana cikin masu neman takarar shugaban kasa a karkashin PDP, ya yi kira na musamman ga jam’iyyar hamayyar.

Premium Times ta rahoto Sanata Anyim Pius Anyim ya na cewa dole ne jam’iyyar PDP ta girmama tsarin karba-karba idan har ta na son lashe zabe.

Anyim Pius Anyim ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake zantawa da mutanen jihar Filato da ya ziyarci garin Jos a yunkurin ganin ya samu tikiti.

Kara karanta wannan

Jerin shugabannin da suka yi nasara, da wadanda suka sha kasa a zaben jam’iyyar APC

Tsohon shugaban majalisar dattawan kasar yana ganin akwai bukatar a 2023 mulki ya koma hannun ‘yan kudu domin a rika tafiya da kowa a siyasa.

Anyim ya soki masu ganin dole sai ‘dan takara ya fito daga Arewa sannan PDP za ta iya cin zabe. ‘Dan siyasar ya ce masu wannan ra’ayin sun yi kuskure.

Ya wajaba a 2023 a fito da ‘dan takara daga kudu, idan ba haka ba, ba zai yiwu a ci zabe ba. Anyim ya ce dalilinsa shi ne lashe zabe sai da adalci da daidaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Dan takarar Shugaban kasa a PDP
Sanata Anyim Pius Anyim Hoto: @anyimpiusa
Asali: Twitter

Dole ne a rika yin karba-karba

Sanata Anyim wanda ya rike kujerar sakataren gwamnatin tarayya a lokacin mulkin Goodluck Jonathan ya ce kowane bangare yana bukatar ‘danuwansa.

Ganin babu wani yanki da zai iya fito da shugaban kasa shi kadai, shiyasa jam’iyyar PDP ta kawo tsarin karba-karba tsakanin Kudu da Arewa cikin dokar ta.

Kara karanta wannan

Masu neman mulkin Najeriya a PDP sun karu, Gwamnan Ribas ya shirya gwabzawa

Vanguard ta rahoto Anyim yana cewa akwai bukatar a samu zaman lafiya da cigaba a jihar Filato, har ya yi alkawarin bunkasa jihar idan ya samu mulkin kasa.

Shugaban PDP ya kai rokonsa

Shugaban jam’iyyar PDP na reshen jihar Filato, Chris Hassan ya karbi jigon na PDP da hannu-biyu, ya ce kowa ya san cewa zai iya rika shugabancin kasar nan.

Chris Hassan ya yi kira ga Anyim da ya dauki akalla mutumin jihar Filato daya a cikin kwamitin yakin neman zabensa ta yadda zai tuna da su idan ya ci zabe.

Tinubu ya yaba da zaben APC

An ji Bola Ahmed Tinubu ya yi wa sababbin ‘Yan Majalisar NWC huduba, ya ce dole su yi kokari wajen ganin an sake samun nasara kan jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Jagoran na jam’iyyar APC ya bayyana inda suka zo daya da Abdullahi Adamu, ya yabawa shugaban kasa da kwamitin CECPC kan zaben shugabanni da aka yi.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Okorocha ya ce ya kamata Tinubu ya hakura ya bar masa tikitin APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel