Takarar 2023: Matasa sun yi karo-karo, sun lale N40m, sun sayawa Bukola Saraki fam a PDP

Takarar 2023: Matasa sun yi karo-karo, sun lale N40m, sun sayawa Bukola Saraki fam a PDP

  • Wasu matasa sun hadu sun saye fam domin Bukola Saraki ya yi takarar shugaban kasa a PDP a 2023
  • Daga mai N200, 000 da N500, 000 zuwa N2m, wadannan matasa sun hada N40m, sun sayawa Saraki fam
  • Tsohon shugaban majalisar dattawan ya yi alkawari zai ba matasa kujerun Minista idan ya samu mulki

Abuja - Wata kungiya ta kwararrun matasa ta sayawa Bukola Saraki fam din sha’awa da neman tsayawa shugaban kasa domin ya yi takara a zaben 2023.

Jaridar Daily Trust ta ce a ranar Litinin, 21 ga watan Maris 2022, wadannan matasa suka yanki fam domin Bukola Saraki ya nemi kujerar shugaban kasa.

Wannan kungiya ta ce ta cin ma wannan matsaya ne domin ta fahimci babu ‘dan siyasar da zai iya shawo kan matsalar matasan kasar nan sai Bukola Saraki.

Kara karanta wannan

2023: Saraki, Tambuwal da ‘Yan takaran Arewa za su hada kai, domin tsaida mutum 1 a PDP

Abubakar Danmusa shi ne shugaban wannan kungiya ta magoya bayan tsohon gwamnan na Kwara. Danmusa ya ce sun yi imani Saraki zai iya kawo gyara.

Bukola Saraki ya jinjinawa masoyansa a kan yadda suka hada wadannan makudan kudi domin su saya masa fam. PDP ta na saida wannan fam a kan N40m.

Fam ba tare da kudinsa ya yi ciwo ba

Da yake jawabi, jaridar ta ce Saraki ya ce hakan yana nufin kira ake yi masa ya tsaya takara.

Bukola Saraki
Dr. Bukola Saraki Hoto: Facebook
Asali: Facebook

“Abin da ku ka yi sako ne gare ni cewa in shiga cikin ‘yan jam’iyyarmu; jagorori da masu zabe da sauran masu ruwa da tsaki domin in samu tikitin takara.
“Sannan kuma in dage har in samu nasara a babban zaben shugaban kasa a watan Fubrairun 2023.”

Kara karanta wannan

Bode George: Zan tattara na koma Ghana sannan na dunga kallo daga nesa idan Tinubu ya zama shugaban kasa

“Aikin da ku ka hada ni da shi, shi ne in yi kira ga duk ‘Yan Najeriya; matasa da tsofaffi, Arewa da Kudu, Kiristoci da Musulmai da wasunsu, masu aikin gwamnati da ‘yan kasuwa, da sauran ‘yan wasu jam’iyyu, mu hada kai domin a gyara Najeriya.”

- Bukola Saraki

Saraki ya yi wa matasa alkawari

Daily Post ta rahoto tsohon shugaban majalisar dattawan yana cewa tun da aka yanko masa fam, babu yadda ya iya illa ya saurari kiransu, ya shiga takara.

Ganin matasa sun kai 62% na Najeriya mai mutane sama da miliyan 200, Saraki ya yi alkawari cewa idan ya samu mulki zai ba matasa kananan Ministoci.

Shirin 2023 a PDP

An ji cewa Bukola Saraki, Bala Mohammed, da Aminu Tambuwal sun yi zama a kan yadda za ta fishe su a zaben tsaida 'dan takarar shugaban kasa a PDP.

‘Yan takarar za su yi zama domin shawo kan Atiku Abubakar da nufin a fito da daya daga cikinsu.

Kara karanta wannan

Ku tara min kudi na gaji Buhari: Dan takara na neman tallafin 'yan soshiyal midiya

Asali: Legit.ng

Online view pixel