Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta fasa taron majalisar zartaswar gobe

Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta fasa taron majalisar zartaswar gobe

  • Yan mintuna bayan haduwa da Buhari, Mai Mala Buni ya soke zaman majalisar FEC na jam'iyyar APC
  • Jam'iyyar ta shirya gudanar da zaman majalisar zartaswa gobe Alhamis ta yanar gizo
  • Shugaba Buhari ya bukaci daukacin gwamnonin jam'iyyar APC su bar Buni ya sha iska kuma ya koma kujerarsa

Birnin tarayya Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta fasa zaman majalisar zartaswar da ta shirye yi gobe Alhamis, 17 ga watan Maris, 2022.

Sakataren kwamitin rikon kwarya, Senator John James Akpanudoedehe, ya sanar da hakan a jawabin da rattafa hannu da yammacin Alhamis, 16 ga Marsi, 2022.

Yace ya sanar da hakan ne bisa umurnin Shugaban kwamitin rikon kwaryan kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, wanda yanzu haka yana birnin Landan tare da Buhari.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Ku bari Buni ya gudanar da taron gangamin jam'iyyar APC, Buhari ya aike da wasika

Yace:

"Bisa umurnin Shugaban kwamitin rikon kwarya da shirya taron gangami ta jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kuma Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, an fasa taron majalisar zartaswar da aka shirya yi ranar Alhamis, 17 ga Maris, 2022."

Mai Mala Buni
Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta fasa taron majalisar zartaswar gobe Hoto: Mai Mala Buni
Asali: Facebook

Ku bari Buni ya gudanar da taron gangamin jam'iyyar APC, Buhari ya aike da wasika

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a bari gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya gudanar da taron gangamin jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

A wasikar da ya aikewa Shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu, Buhari yace gudun shiga rikice-rikicen kotu, a bari Buni ya karasa aikinsa.

Buhari yace:

"Na samu labarin cewa sakamakon abubuwan da suka faru, APC na fuskantar kasa-kasai a kotu a fadin tarayya."

Kara karanta wannan

Labarin cikin Hotuna: Mai Mala Buni yayi takakkiya zuwa Landan don ganin Shugaba Buhari

"Sakamakon haka, akwai yiwuwan hukumar INEC ta hana jam'iyyar gudanar da ayyukanta."
"Saboda haka, a bari Mai Mala Buni da sauran mambobin kwamitinsa su cigaba da shirye-shiryen taron gangamin ranar 26 ga Maris, 2022."

Asali: Legit.ng

Online view pixel