Primate Ayodele ya bayyana abun da zai samu APC da PDP gabannin 2023

Primate Ayodele ya bayyana abun da zai samu APC da PDP gabannin 2023

  • Primate Ayodele ya yi hasashen cewa babban taron APC zai gamu da cikas idan har ba a saisaita abubuwa ba
  • Limamin cocin ya kuma yi hasashen cewa kokarin gwamnoni na daidaita abubuwa zai sake haifar da rikici a jam’iyyar
  • Ya kuma bayyana cewa jam’iyyar PDP za ta hadu da nata matsalolin gabannin babban zaben 2023

Babban limamin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya saki sabon hasashe game da babban taron jam’iyyar All Progressive Congress (APC) da rikicin people democratic party (PDP).

A wata sanarwa dauke da sa hannun hadimin labaransa, Osho Oluwatosin, Primate Ayodele ya bayyana cewa babban taron APC zai yi sanadiyar rugujewar jam’iyyar mai mulki idan ba su daidaita abubuwa ba.

Ya bayyana cewa korarren shugaban rikon kwarya, Mai Mala Buni ba zai ga rahamar wasu gwamnoni ba, sannan cewa yunkurin gwamnoni na saisaita abubuwa zai kara haddasa rikici cikin jam’iyyar, PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Saura kwanaki 11 a shirya zaben shugabanni, kan jam’iyyar APC ya kara tarwatsewa

Primate Ayodele ya bayyana abun da zai samu APC da PDP gabannin 2023
Primate Ayodele ya bayyana abun da zai samu APC da PDP gabannin 2023
Asali: Original

Babban faston wanda ya yi hasashen dage babban taron da kuma baraka a jam’iyyar mai mulki, ya bayyana cewa abubuwa da dama za su tabbatar da wanda zai zama shugaban APC na gaba kuma na kusa da shugaban kasa Muhammadu Buhari za su taka rawa a hukuncin da zai zartar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bugu da kari, ya yi gargadin cewa akwai gagarumin matsala da zai tunkaro gabannin taron na APC domin zababben shugabanta na kasa zai haifar da bangarori a tsakanin jam’iyyar kuma zai yi sanadiyar ficewar wasu yan siyasa.

Ya ce:

“Dole APC ta yi taka-tsan-tsan a babban taronta mai zuwa saboda zai ruguza jam’iyyar idan basu saisaita abubuwa ba. Buni ba zai ga rahama daga wasu mutane ba kuma ya zama dole gwamnoni su yi hankali saboda daidaita wasu abubuwan zai kuma haddasa rikici a jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Ɗiyar Bola Tinubu ta yi tsokaci kan shirin mahaifinta na gaje kujerar Buhari

“Abubuwa da yawa za su kai ga tabbatar da shugaban APC na kasa na gaba, manyan yan siyasa biyu za su kasance a takarar kuma na kewaye da shugaba Buhari za su taka rawa a hukuncin da zai zartar. Na kewaye da shugaban kasar ne za su zabi shugaban APC da dan takarar shugaban kasa na gaba.
“Akwai wani gagarumin matsala da zai tunkaro gabannin babban taron APC kuma mutane da dama za su ji babu dadi, mutumin da za a zaba a matsayin shugaban jam’iyyar zai haifar da bangarori a cikin jam’iyyar, wannan zai hana wasu mutane dawowa harkar siyasa.”

Wasu mutane na kokarin ruguza PDP

A bangaren PDP, Primate Ayodele ya bayyana cewa wasu gwamnoni na son ruguza jam’iyyar kuma akwai bukatar su yi hankali domin kada su yi batan kai a zabe mai zuwa.

Ya bayyana cewa wasu za su wahalar da shugaban jam’iyyar na kasa, Mista Ayu a cikin jam’iyyar koda dai zai yi kokarin saita jam’iyyar kan tafarki madaidaiciya, ba za a gode masa ba.

Kara karanta wannan

Na kusa da Buhari ga Osinbajo da Fayemi: Tinubu ya fi karfinku a zaben 2023, ku hakura kawai

Ya bayyana cewa za a yi masa bita da kulli, a kaskantar da shi kamar yadda suka yiwa tsohon shugaban jam’iyyar, Uche Secondus amma ta wani salo.

Ya kuma gargadi wasu gwamnoni da su nemi hasken Ubangiji wajen zabar magadansu domin kada a ci amanarsu.

“Ya zama dole wadannan gwamnonin su yi hankali wajen zabar magadansu; Nyesom Wike, Ifeanyi Okowa, Ifeanyi Ugwuanyi, idan ba su nemi zabin Allah ba, za a ci amanar su.”

Ba zai taba zama shugaban kasa ba, Fasto ya yiwa gwamnan wata jiha baki

A wani labarin kuma, mun kawo a baya cewa babban limamin cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya ce gwamnan jihar Ribas, Nyesome Wike, ba zai taba zama shugaban kasar Najeriya ba.

Faston ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakinsa, Osho Oluwatosin, ya saki a ranar Talata, 25 ga watan Janairu.

Malamin addinin ya kuma yi gargadin cewa Wike zai rusa jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) idan shugabannin jam'iyyar adawar ba su gyara abubuwa ba, PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sauya sheka: APC na neman a hana Saraki, Tambuwal, Ortom da sauransu yin takara na shekaru 30 a sabon kara

Asali: Legit.ng

Online view pixel