Yadda Fayose ya hango rikicin da ya barkowa PDP a yanzu tun shekaru 2 da suka wuce

Yadda Fayose ya hango rikicin da ya barkowa PDP a yanzu tun shekaru 2 da suka wuce

  • Tun a 2020 Ayodele Peter Fayose ya yi hasashen cewa ba za a kwashe lafiya da Godwin Obaseki ba
  • Tsohon gwamnan jihar Ekiti ya ce Gwamna Godwin Obaseki zai juyawa su Nyesom Wike baya a PDP
  • Kusan shekaru biyu da Fayose ya yi wannan magana, cacar baki ta kaure tsakanin Wike da Obaseki

Ekiti - A shekarar 2020, Mista Ayodele Fayose ya yi wani hasashe wanda kuma ya zama daidai a game da rikicin cikin gidan jam’iyyar hamayya ta PDP.

Legit.ng za ta iya tuna cewa Ayodele Fayose ya hango rana irin ta yau, inda ya ce za a samu rashin jituwa tsakanin Nyesom Wike da kuma Godwin Obaseki.

A halin yanzu wadannan gwamnoni biyu na PDP su na ta maidawa junansu martani. Tun shekaru biyu da suka wuce, Fayose ya ce za a ga wannan rana.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Gwamnoni biyu sun barke da rikici mai zafi, sun fara kiran juna 'Ma ci Amana'

A wannan bidiyon da aka bankado, za a ji ‘dan siyasar yana cewa bayan Obaseki ya samu tazarce a PDP, zai yi rigima da wasu wadanda suka taimaka masa.

Tsohon gwamnan na jihar Ekiti ya kama sunan Nyesom Wike, ya ce gwamnan Edo yana cikin wadanda zai yaka da zarar ya cin ma bukatarsa na zarcewa.

Da APC ta hana Obaseki takara, PDP ce ta rufa masa asiri, ta bashi tikiti, kuma ya samu tazarce.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Obaseki
Gwamna Godwin Obaseki da Gwamna Nyesom Wike Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Abin da Ayo Fayose ya fada

“Ba zan yi mamaki ba, Obaseki zai yi nasara a wannan zaben saboda Oshiomhole ba mutumin kirki ba ne.”
“Amma idan ya lashe wannan zabe, ba zan yi mamaki ba idan ya dawo kan abokina, Wike da makamantansu.”
“Su na yi masa yaki, amma ku tuna na fadi maganar nan, ina fata Obaseki ba zai sa a tuno da bidiyon nan ba.”

Kara karanta wannan

Rikici ya kara tsanani tsakanin gwamnonin PDP, sun fara nuna wa juna yatsa

“Saboda dole ne ya cika alkawarin da ya yi masu, domin sun rike jam’iyyar ne saboda zuwansa.”

- Ayo Fayose

Adams Oshiomhole v Godwin Obaseki

A lokacin da Fayose ya yi wannan magana, ana rigima tsakanin Obaseki da shugaban jam’iyyar APC na kasa (na wancan lokaci) watau Adams Oshiomhole.

Sabanin Obaseki da tsohon uban gidansa ne ya jawo aka hana shi tikitin takara a karkashin APC. A karshe dai wannan rikici ya ci APC, aka sauke Oshiomhole.

Kwamacala a gidan jam'iyyar APC

Ana daf da zaben shugabannin APC, amma an ji ‘yan takara su na ta rigima, gwamnoni sun gagara hada-kai, kwamitoci ba su zauna ba, ba a fara saida fam ba.

Yayin da Muhammadu Buhari ya je Landan, Mai Mala Buni yana Dubai inda ya je ganin likita. Sannan kuma uwar jam’iyya tana fama da wasu shari’o’i a kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel