2023: Gwamnan Bauchi ya kai wa Obasanjo ziyara har gida

2023: Gwamnan Bauchi ya kai wa Obasanjo ziyara har gida

  • Sanata Bala Mohammed ya kai ziyara har gidan tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo a Abeokuta, jihar Ogun
  • Bala Mohammed ya ce ya je neman shawara ne wurin Obasanjo domin babu abinda zai iya aiwatarwa babu saninsa
  • A cewar gwanan Bauchin kuma tsohon ministan Abujan, ya na da tabbacin shi ne zai yi wuf da tikitin takarar shugabancin kasa a PDP

Abeokuta, Ogun - Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed a ranar Laraba ya yi ganawar sirri da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a Abeukuta, babban birnin jihar Ogun.

Mohammed ya na daya daga cikin masu hararo kujerar shugaban cin kasa a 2023 karkashin jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, Daily Trust ta ruwaito.

2023: Gwamnan Bauchi ya kai wa Obasanjo ziyara har gida
2023: Gwamnan Bauchi ya kai wa Obasanjo ziyara har gida. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Tsohon ministan babban birnin tarayyan tare da hadimansa sun isa gidan Obasanjo da ke dakin karatu na Olusegun Obasanjo a Abeokuta wurin karfe 11.30 na safe kuma kai tsaye suka shiga ganawar sirri ta tsawon sa'a daya da Obasanjo.

Kara karanta wannan

Shin za ka tsaya takara a 2023: Jonathan ya ba da amsar da ba a yi tsammani ba

A yayin ganawa da manema labarai, Mohammed ya yi bayanin cewa ya gana da Obasanjo ne kan burinsa kafin zuwan 2023.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Gwamnan ya jaddada cewa ya dace shugabancin Najeriya ya kasance saboda nagarta ne.

Gwamnan ya jaddada cewa yana sa ran samun tikitin takara karkashin jam'iyyar PDP, inda yace Najeriya ta yi girman da bai dace a yi burus da ita ba.

Ya ce:

"Kuma na zo ne domin in tattauna kan wasu burika nawa saboda ba zan iya komai ba ba tare da na fada masa ba. Dalili kuwa shi ne ya na da matukar amfani gare mu baki daya.
"Abinda mu ke kokarin yi a jam'iyyarmu shi ne, mun san mai ruwa da tsaki ne amma muna sake gina jam'iyyar ne, muna kuma bukatar shi. Kalamansa masu daraja suna da matukar amfani. Don haka na zo jin ta shi ra'ayin ne kan wasu abubuwa da za mu yi a jam'iyyarmu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Yadda jami'in dan sanda ya mutu a cikin gidan wani tsohon gwamna

"Muna so mu bayar da dama ga 'yan Najeriya da za su iya ceto kasar daga halin da ta fada da kuma rabuwar kan da muka tsinci kanmu a ciki. Wadannan su ne manyan dalilai biyu da na zo gare shi."

Na sanar da Atiku cewa ya tsufa kuma gajiye ya ke, ba zai iya shugabanci ba, Gwamnan Bauchi

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce ya fada wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubukar ya bar neman kujerar shugabancin kasa saboda ya tsufa da yawa kuma a gajiye yake da daukar ragamar Najeriya.

Ya fadi hakan ne a wani jawabi da yayi yayin amsar rahoton kwamitin tuntuba da ya samar na burin sa na tsayawa takarar shugaban kasa wanda ya gudana a ranar Juma'a a tsohon dakin taron Banquet a gidan Gwamnatin Bauchi.

Sunday Punch ta ruwaito yadda kwamiti karkashin jagoranci Adamu Gumba, wanda aka kaddamar a 15 ga Agusta, 2021, bayan ziyartar jihohin arewa 16 inda ta yi hulda da masu rike da mukamai daban-daban a wadannan jihohin.

Kara karanta wannan

Mulki ba naku bane: Obasanjo ya shawarci tsoffin da ke neman tsayawa takara a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel