2023: An gano inda Obasanjo da manyan Janarori suka karkata, sun yi watsi da Atiku

2023: An gano inda Obasanjo da manyan Janarori suka karkata, sun yi watsi da Atiku

  • Akwai rade-radin cewa Cif Olusegun Obasanjo da tsofaffin sojoji sun watsar da Atiku Abubakar
  • Tsohon shugaban na Najeriya ya na sha’awar shugabancin kasar nan ya bar Arewa a zaben 2023
  • Idan ‘Yan Kudu za su karbi shugabanci, ‘Yan takarar Obasanjo sun hada da Dr. Akinwumi Adesina

Nigeria - Alamu su na nuna cewa tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo da wasu tsofaffin sojojin kasa su na goyon bayan mulki ya koma kudu a 2023.

A ranar 14 ga watan Fubrairu 2022 ne jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa Olusegun Obasanjo da wasu abokan aikinsa su na da ‘yan takarar shugaban kasa.

Daga cikin wadanda suke marawa baya su karbi mulkin Najeriya a zabe mai zuwa akwai shugaban bankin nan na cigaban Afrika, Dr. Akinwumi Adesina.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa: Buhari ya yi ganarwar sirri da TY Danjuma da Mohammed Indimi

Har ila yau ana kishin-kishin cewa manyan kasar su na tare da tsohon gwamna Peter Obi da kuma tsohon mataimakin shugaban CBN, Farfesa Kingsley Mohgalu.

Wani na kusa da tsohon shugaban Najeriyan da tsofaffin Janar na sojoji ya shaidawa jaridar cewa manyan kasar ba su tare da Atiku Abubakar a zaben na 2023.

Obasanjo
Buhari tare da su Obasanjo Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

An kawo maganar Farfesa Jega

Ana kuma samun kishin-kishin cewa tsohon shugaban hukumar zabe na kasa watau INEC, Farfesa Attahiru Jega suke so a mataimakin shugaban kasa.

“Shi Obasanjo ya na goyon bayan mulki ya koma kudu. Mutanen da yake sha’awa su samu mulki su ne; Akinwumi Adesina, Peter Obi da Kingsley Moghalu.”
“A yankin Arewa kuma, ya (Obasanjo) na kaunar Attahiru Jega (tsohon shugaban hukumar INEC), ya zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa.”

Kara karanta wannan

2023: Hotunan ziyarar da manyan jiga-jigan PDP suka kaiwa tsohon shugaban kasa, IBB

“Bai tare da Atiku Abubakar ko kadan. Ya na goyon bayan mulki ya bar Arewa.” - Majiyar.

Farfesa Jega ne ya jagoranci shirya zabukan da aka yi a 2011 da 2015. Bayan ya sauka daga mukaminsa, malamin jami’ar ya shiga siyasa domin kawo gyara.

Tambuwal ya dage

Kun ji cewa domin ganin ya samu damar kai labari a zaben 2023, gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal ya ziyarci Ahmad Muhammad Makarfi har gidansa.

Aminu Tambuwal ya yi zama da Sanata Ahmad Makarfi ne a matsayinsa na jigo a tafiyar PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel