Fadar Shugaban kasa: Buhari ya yi ganarwar sirri da TY Danjuma da Mohammed Indimi

Fadar Shugaban kasa: Buhari ya yi ganarwar sirri da TY Danjuma da Mohammed Indimi

  • Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da Janar Theophilus Yakubu Danjuma a Aso Rock a ranar Talata, 8 ga watan Fabrairu
  • Shugaban na Najeriya ya kuma gana da hamshakin attajirin nan Alhaji Mohammed Indimi a fadar shugaban kasa
  • Ba a bayyana cikakkun bayanai kan ganawar biyu da aka bayyana a zaman na sirri ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto

Aso Rock, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 8 ga watan Fabrairu ya karbi bakuncin tsohon ubangidansa na soji, Janar Theophilus Yakubu Danjuma a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa da ke Abuja.

Ba a bayyana manufar ganawarsa da Danjuma ba, duk da cewa an ga hotunan da mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ya fitar a shafinsa na Facebook da Legit.ng ta gani.

Kara karanta wannan

2023: Hotunan ziyarar da manyan jiga-jigan PDP suka kaiwa tsohon shugaban kasa, IBB

Ganawar Buhari da hamshakan manyan Najeriya
Fadar Shugaban kasa: Buhari ya yi ganar sirri da TY Danjuma da Mohammed Indimi | Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Adesina yace taron na sirri ne tsakanin shugaba Buhari da TY Danjuma.

A cewar Adesina, shugaba Buhari ya kuma tarbi gawurtaccekuma hamshakin attajirin nan Alhaji Mohammed Indimi, a wata ganawar ta sirri.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli hotuna:

2023: Gwamnonin arewa biyu sun garzaya fadar shugaban kasa, sun saka labule da Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ranar Talata, ya karbi bakuncin gwamnonin jam'iyyar APC guda biyu a fadarsa dake babban birnin tarayya Abuja.

Daily Trust ta rahoto cewa gwamnonin sune, Atiku Bagudu na jihar Kebbi, shugaban kungiyar gwamnonin APC a karo na biyu, da kuma Muhammad Badaru na jihar Jigawa.

Gwamnonin sun gana da shugaban kasa Buhari ne dangane da babban gangamin APC na kasa dake tafe ranar 26 ga watan Fabrairu, wanda za'a zabi shugabannin jam'iyya a matakin kasa.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Okorocha ya gana da Buhari kan kudirinsa na son zama magajinsa

A ranar Alhamis da ta gabata, jam'iyyar APC ta rantsar da sabbin shugabanninta na jihohi yayin da take fuskantar babban taro.

A wani labarin, daya daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki, Daniel Bwala, ya yi ikirarin Farfesa Yemi Osinbajo ba zai yi takara da Asiwaju Bola Tinubu ba.

Daniel Bwala ya bayyana wannan ne a lokacin da aka gayyace shi ya yi magana a gidan talabijin nan na Channels TV a ranar Talata, 8 ga watan Fubrairu 2022.

Bwala ya fito karara yana cewa mataimakin shugaban kasar ba zai ja da tsohon mai gidansa da yake fashin baki a cikin shirin siyasa na Politics Today a jiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel