‘Yan PDP a Majalisa sun tsaida wanda suke goyon baya ya nemi takarar Shugaban kasa

‘Yan PDP a Majalisa sun tsaida wanda suke goyon baya ya nemi takarar Shugaban kasa

  • Anyim Pius Anyim ya samu goyon bayan ‘yan PDP a majalisa a neman takarar shugaban kasarsa
  • ‘Yan majalisar kasar sun nuna su na tare da tsohon sakataren gwamnatin tarayyar a zaben 2023
  • Sanata Eyinnaya Abaribe ya fadawa Sanata Pius Anyim ka da ya ja da baya sai ya kai ga burinsa

Abuja - Bangaren marasa rinjaye a majalisar tarayya sun yi wa Anyim Pius Anyim mubaya’a a kan neman tikitin takarar shugaban kasa da ya sa a gaba.

A wani rahoto da Daily Trust ta fitar a ranar Alhamis, 10 ga watan Fubrairu 2022, an ji cewa ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP a majalisar tarayya sun yi wani zama.

A karshen wannan zama da aka yi a katafaren otel dinnan na Transcorp Hilton a Abuja, ‘yan majalisar sun nuna su na goyon bayan Anyim Pius Anyim.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar PDP ta tafka kasurgumar asara a Majalisa bayan rasa Sanatoci 6 a shekara 1

Sanata Anyim Pius Anyim ya sanar da ‘yan majalisar niyyarsa na neman takarar shugaban kasa.

Tsohon shugaban majalisar kasar ya fadawa ‘yan majalisar cewa ba zai iya cin ma wannan buri na shi ba tare da taimakonsu a matsayinsa na mutanensa ba.

Jaridar Punch ta rahoto Pius Anyim ya na cewa ya ga bukatar ya fadawa ‘yan majalisa shirin takarar da yake yi da kansa, kafin ya same su daya bayan daya.

Fadar Shugaban kasa
Anyim Pius Anyim a taron FEC Hoto: www.informationng.com
Asali: UGC

“Ba zan iya kai labari ni kadai ba. Amma idan mutanen da za su taimaka mani, su ka fada mani cewa in dakata, dole in tsaya a inda ku ka ce in tsaya.”
“Amma idan a yau ku ka fada mani cewa in sa kai, ku tabbatar cewa zan sa gaba domin mu fafata. Duk abin da ya faru, zan tuna kun mara mani baya.”

Kara karanta wannan

2023: Dalilai 2 da suka sa Farfesa Osinbajo ba zai yi takara da Bola Tinubu ba - Jigon APC

- Anyim Pius Anyim

Mu na tare da kai - Eyinnaya Abaribe

Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Eyinnaya Abaribe ne ya yi magana a madadin abokan aikinsa, ya nuna masa cewa duk su na tare da shi.

A cewar Sanatan na PDP, ‘yan majalisa su na kokari idan suka rike madafan iko, don haka ya karfafa neman tikitin takarar tsohon shugaban majalisar dattawan.

“A madadinmu hadakar ‘yan majalisa, mu na cewa ka da ka ja da baya, ka jajirce a wannan tafiya domin ka zama shugaban kasar Najeriya.” - Eyinnaya Abaribe.

Tambuwal ya dage

Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya sha alwashi gwamnatinsa za ta inganta harkar tsaro ta hanyar samar da kayan makamai na zamani idan ya samu mulki.

Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya ce zai tabbatar an samu isassun kayan aiki na zamani, sannan zai dage wajen kula da walwalar jami’an tsaro a matsayin shugaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel