Ana tare: El-Rufai, Ganduje da Gwamnoni 6 da suka taba mika mulki ga Mataimakansu

Ana tare: El-Rufai, Ganduje da Gwamnoni 6 da suka taba mika mulki ga Mataimakansu

  • Gwamna Darius Ishaku ya taba shafe kimanin watanni uku ba ya Taraba. Amma duk tsawon wannan lokaci bai mika mulki ga mataimakinsa ba
  • Amma akwai wasu gwamnoni da suke yin akasin abin da Gwamna Darius Ishaku ya yi, su kan bada rikon mulki na rikon kwarya idan har ba su gari
  • Haka ta faru da gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu lokacin da ya kamu da cutar COVID-19 a 2021, ya ki ba Agboola Ajayi daman rike gwamnati

Abin da doka ta ce shi ne Gwamna ya mika mulki ga mataimakinsa idan ba ya ofis. Gwamnan zai yi hakan ne ta hanyar aika takarda ga majalisar dokoki

A wannan rahoto, Legit.ng ta kawo jerin Gwamnonin da suka taba mikawa mataimakansu mulki:

Kara karanta wannan

Babu wani amfani: Masari ya nemi a bude iyakokin Katsina yadda aka bude na sauran Jihohi

1. Nasir El-Rufai

Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya saba barin jihar Kaduna a hannun mataimakansa. An yi haka a lokacin Barnabas Yusuf Bala yana mataimakinsa.

Musamman lokacin da yake karatun PhD a kasar waje, Malam El-Rufai yana bada aron mulki, har an taba yin lokacin da Hon. Aminu Shagali ya ke rike da jihar.

2. Abdullahi Sule

A 2020 Mai girma Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa bar mataimakinsa ya zama gwamnan rikon kwarya a lokacin da ya je ganin likita a Amurka.

Gwamna Sule ya sanar da majalisar jiha game da tafiyarsa, ya bar mataimakinsa ya rike jihar.

El-Rufai, Ganduje da Gwamnonin jihohi
Gwamnonin da su ka taba bada mulki Hoto: @GovKaduna, @NasarawaGovt, @ProfZulum, @RotimiAkeredolu, @GovernorIkpeazu
Source: UGC

3. Babagana Umara Zulum

An yi lokacin da Usman Kadafur ne yake jan ragamar gwamnatin jihar Borno, a lokacin da Mai girma Farfesa Babagana Umara Zulum ya je hutun kwana 21.

Kara karanta wannan

Gyadar doguwa: Gwamna ya canza rayuwar 'yan mata 2 daga haduwa da su a hanyar kauye

Kafin ya je hutun, Gwamna Babagana Umara Zulum ya aikawa majalisar dokokin Borno takarda.

4. Rotimi Akeredolu

Kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, gwamnan Rotimi Akeredolu ya kyale Lucky Orimisan Aiyedatiwa ya zama gwamnan rikon kwarya a 2021.

Akasin abin da ya faru da yake rigima da Agboola Ajayi, Akeredolu yana ba Aiyedatiwa dama.

5. Okezie Ikpeazu

A watan Yunin 2020, Mai girma gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia ya sanar da Duniya cewa ya kamu da cutar COVID-19, hakan ta sa ya killace kan shi a gida.

Okezie Ikpeazu ya bar mataimakin Gwamnan jihar Abia, Rt Hon Ude Oko Chukwu ya zama gwamnan rikon kwarya a lokacin da yake jinya kafin ya samu lafiya.

6. Abdullahi Umar Ganduje

A Disamban shekarar bara Nasir Gawuna ya zama gwamnan rikon kwarya a jihar Kano. Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya mika masa ragamar mulki da ya bar kasar.

Gwamna Ganduje ya bar jihar a hannun Nasiru Gawana da ya je yin kwas a jami’ar Harvard da ke kasar Amurka. Ba wannan ne karon farko da Ganduje ya mika mulki ba.

Kara karanta wannan

Sabon lale: Atiku ya jefar da abokin takararsa, zai zabi Gwamnan PDP ya yi masa mataimaki

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng