Zargin siyasa: Majalisa ta tabbatar da nadin kwamishinan INEC da ake zargin yar APC ce

Zargin siyasa: Majalisa ta tabbatar da nadin kwamishinan INEC da ake zargin yar APC ce

  • Majalisar dattawa a ranar Laraba, 2 ga watan Fabrairu, ta tabbatar da Rhoda Gumus a matsayin kwamishinar INEC daga kudu maso kudu
  • Hakan na zuwa ne bayan kungiyar HURIWA ta shigar da korafi majalisa kan zargin cewa Gumus yar APC ce
  • Sai dai shugaban kwamitin majalisa kan INEC, Kabiru Gaya, ya ce basu samu kowani korafi kan Gumus ba kafin gabatar da rahotonsu

Abuja - Jaridar The Cable ta ruwaito cewa majalisar dattawa ta tabbatar da Rhoda Gumus a matsayin kwamishinar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) daga kudu maso kudu.

Hakan na zuwa ne duk da rade-radin da ake yi na cewa Gumus wacce aka zaba daga jihar Bayelsa ta kasance mamba a jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Sule Lamido ya ce Tambuwal ne ya fi dacewa ya gaji Buhari, ya fadi dalili

Kafin rantsar da Gumus, kungiyar kare hakkin dan adam ta HURIWA, ta mika takardar korafi gaban shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan kan nadin nata.

Zargin siyasa: Majalisa ta tabbatar da nadin kwamishinan INEC da ake zargin yar APC ce
Zargin siyasa: Majalisa ta tabbatar da nadin kwamishinan INEC da ake zargin yar APC ce Hoto: Arise News
Asali: UGC

A takardatr korafin mai kwanan wata 26 ga watan Janairu zuwa ofishin shugaban majalisar, jagoran kungiyar HURIWA ta kasa, Emmanuel Onwubiko, ya ce sun sami takardun da ke tabbatar da cewar Gumus na dauke da katin shaidar kasancewa yar jam'iyyar mai mulki.

Sun sanya kwafin takardun a korafin da suka shigar.

Sai dai kuma, yayin da yake gabatar da wani rahoto a zauren majalisar a ranar Laraba, 2 ga watan Maris, Kabir Gaya, shugaban kwamitin INEC, ya ce ba a sami kowani korafi kan Gumus ba.

Gaya ya ce:

"An yiwa wadanda aka zaba tambayoyi kuma sun amsa sosai. Ya shugaba, mun samu korafi daya ne kawai game da Manjo Janar Alkali.

Kara karanta wannan

An yankewa Hedmasta hukuncin share filin kwallo tsawon wata 3 kan satar kudin makaranta

"Amma ta kafofin watsa labarai, bayan mun gabatar da rahotonmu, sai muka sake jin labarai game da wata daban (Gumus). Kwamitin ya samu wani korafi daga dattawan Taraba kan Alikali."

Gaya ya ce dattawan na so matsayin na arewa maso gabas ya je jihar Taraba. Sai dai, ya ce mambobin kwamitin sun yi watsi da korafin saboda shugaban kasa na da damar zabar duk wanda yake so daga kowace jiha a arewa maso gabas.

Sauran wadanda aka tabbatar a matsayin kwamishinonin INEC sune Mohammed Haruna (arewa ta tsakiya), May Agbamuche-Mbu (kudu maso kudu), Ukeagu Nnamdi (kudu maso gabas), da Sam Olumekum (kudu maso yamma).

Buhari ya sake zabar yar APC a matsayin kwamishinar INEC, HURIWA ta kai kara majalisa

A baya mun ji cewa, Shugaban kasa Muhammdu Buhari ya sake nada yar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin kwamishinar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta.

Kara karanta wannan

Kisan Hanifa: Ganduje ya sake martani kan kisan Hanifa, ya ce dole ne a yi adalci

A watan da ya gabata ne Buhari ya sanar da zabar Rhoda Gumus, farfesar injiniya a jami’ar Niger-Delta domin maye gurbin Lauretta Onochie, hadimarsa a kafofin watsa labarai.

Sauyin ya biyo bayan cece-kucen da zabar Onochie ya haifar, wanda ya ta’allaka ne a kan jam’iyyarta. Don haka majalisar dattawa ta ki amincewa da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel