Babban Dattijon Neja-Delta ya fadi ‘Dan takara 1 daga Arewa da zai iya marawa baya a 2023

Babban Dattijon Neja-Delta ya fadi ‘Dan takara 1 daga Arewa da zai iya marawa baya a 2023

  • Farfesa Iyorwuese Hagher ya sanar da Edwin Kiagbodo Clark shirin Bukola Saraki na shiga takara a 2023
  • Edwin Kiagbodo Clark ya karbi wannan magana, ya ce zai iya goyon bayan Saraki idan babu ‘Dan kudu
  • Solomon Ewuga, Bello Adokwe, da Idem Unyime su na cikin masu taya Saraki samun takarar shugaban kasa

Abuja - Babban ‘dan siyasar Kudu maso kudancin Najeriya, Edwin Kiagbodo Clark ya bada sharadin goyon bayan Bukola Saraki a takarar shugaban kasa.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Cif Edwin Kiagbodo Clark ya fitar da wannan jawabi ne bayan ya hadu da ‘yan majalisar da ke taya Bukola Saraki yakin neman zabe.

Farfesa Iyorwuese Hagher wanda shi ne shugaban majalisar wayar da kan mutane game da takarar shugaban kasar Bukola Saraki ya zauna da Clark a Abuja.

Kara karanta wannan

Ka nemi kujerar Buhari, mun duba maka – Mataimakin Gwamnan PDP ga Osinbajo

A wajen wannan zama, Farfesa Hagher da ‘yan majalisarsa sun fadawa dattijon bukatar a samu hadin-kai a Najeriya ta hanyar tsaida wanda ya san kan al’amura.

Edwin Clark ya bayyana cewa Bukola Saraki ya rike majalisar dattawa da kyau a lokacinsa yayin da Farfesa Iyorwuese Hagher ya sanar da shi burin na takara a 2023.

Bukola Saraki
Sanata Bukola Saraki Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

An rahoto Iyorwuese Hagher yana bada shawarar a samu wanda ya san kan aiki ya zama shugaban kasa. A ganinsu, tsohon gwamnan na Kwara ya cancanta.

Edwin Clark ya yi na'am?

Da yake maida martani, Edwin Clark ya ce shugabancin Najeriya na bukatar wanda ya san kasar.

A cewar Edwin Kiagbodo Clark, idan ba a iya samun ‘dan siyasa daga kudancin Najeriya da ya samu takarar shugaban kasa ba, zai goyi bayan takarar Bukola Saraki.

Kara karanta wannan

Matsayin Da Ake Ciki Akan Sulhu da yan tsagin Gwamna Ganduje, Malam Ibrahim Shekarau

“Mun dade mu na kiran mulki ya koma kudu. Amma idan ba mu iya samun ‘dan takarar da kowa ya yi wa mubaya’a daga kudu ba, babu yadda na iya, dole in goyi bayan Bukola Saraki.”

- Edwin Kiagbodo Clark.

Sauran ‘yan tawagar Saraki sun hada da Sanata Solomon Ewuga, Sanata Bello Adokwe, Hon. Idem Unyime, Hon Moses Aliyu, da sauran jiga-jigan jam’iyyar PDP na kasa.

Osinbajo zai dace a 2023?

Farfesa Yemi Osinbajo ya samu goyon-bayan PDP, Mataimakin Gwamnan jihar Edo, Phillip Shuaib ya ce an daina siyasar Uban gida, don haka su na tare da shi a 2023.

Phillip Shuaib ya ce Mai martaba Osinbajo ya san da cewa ya na da mutanen jihar Edo tare da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel