2023: Ku zaɓi shugabanni masu tsoron Allah, Shawarar gwamnan APC ga 'yan Najeriya

2023: Ku zaɓi shugabanni masu tsoron Allah, Shawarar gwamnan APC ga 'yan Najeriya

  • Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, ya shawarci ‘yan Najeriya da su zabi shugabanni masu tsoron Allah don su jagorance su
  • Gwamnan ya yi wannan kiran ne ta wata takarda da ya bayar a taron shugabannin ‘yan siyasar katolika da ‘yan kasuwa na Abuja da suka yi a garin Jos ranar Juma’a
  • A cewarsa shugaban da yake da tsoron Allah zai kamanta adalci da abubuwan da suka dace kuma hakan zai tallafa don kawo karshen matsalolin da Najeriya ke fuskanta

Filato - Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya bukaci ‘yan Najeriya su zabi shugabanni masu tsoron Allah da girmama jama’a don su wakilce su a ofisoshin gwamnati, The Guardian ta ruwaito.

Gwamnan ya yi kiran ne yayin wani taro na ‘yan siyasar kotolika da shugabannin ‘ya. Kasuwan na Abuja ta wata takarda da Sakataren watsa labaransa, Dr Makuy Machan ya saki a ranar Juma’a a garin Jos.

Kara karanta wannan

2023: Malaman addinin Musulunci da Kirista fiye 1,000 sun yi taron yi wa gwamnan APC addu’o’in samun nasara

2023: Ku zaɓi shugabanni masu tsoron Allah, Shawarar gwamnan APC ga 'yan Najeriya
2023: Gwamna Lalong ya shawarci 'yan Najeriya su zabi shugabanni masu tsoron Allah. Hoto: The Guardian
Asali: Twitter

A cewarsa, tsoron Allah ne zai taimaka wa shugabanni don su yi ayyukan su yadda ya dace cikin adalci ga al’ummar su.

Lalong ya bukaci kowa ya yi zabe

Ya bukaci ‘yan Najeriya masu addinai mabambanta da su tabbatar sun yi zabe, inda yace hakan zai sa burin kowa ya cika.

The Guardian ta nuna inda Lalong ya ce taron zai taimaka wurin samar da hanyoyin tattaunawa da ‘yan siyasa mabiya katolika don su yi abubuwan da zasu taimaka wa kasa.

Kuma a cewarsa hakan zai bayar da damar tattaunawa don sanin hanyoyin kawo garanbawul ga matsalolin da Najeriya ta dade tana fuskanta kamar rashawa, cutuka, talauci da rashin ababen more rayuwa na kwarai.

2023: Za mu bi didigin inda ƴan takara suke samo kuɗi, za mu sa ido kan asusun bankin ƴan siyasa, INEC

Kara karanta wannan

Mukarraban Buhari su na jiran matsayarsa a kan takarar Osinbajo, Tinubu a zaben 2023

A wani rahoton kun ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, INEC, ta aika da muhimmin sako ga yan siyasa da jam'iyyun siyasa gabanin babban zaben shekarar 2023.

Hukumar ta sha alwashin cewa za ta saka idanu a kan 'yan siyasa da jam'iyyun siyasa domin gano inda suke samo kudade domin yakin neman zabe, Vanguard ta ruwaito.

Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana hakan yayin wani taro da hukumar zaben ta shirya a Abuja, ranar Juma'a 21 ga watan Janairu, kuma ya ce hukumar za ta saka ido kan yadda aka hada-hadar kudade ranar zabe don dakile siyan kuri'u, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel