2023: Malaman addinin Musulunci da Kirista fiye 1,000 sun yi taron yi wa gwamnan APC addu’o’in samun nasara

2023: Malaman addinin Musulunci da Kirista fiye 1,000 sun yi taron yi wa gwamnan APC addu’o’in samun nasara

  • Fiye da malamai 1,000 na addinin musulunci da kirista sun taru a Abuja ranar Juma’a inda suka nuna goyon bayan su ga gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello
  • Ba anan suka tsaya ba, sun yi masa addu’o’i tare da fatan shi ne zai maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2023
  • A cewar su, ya yi aiki tukuru a Jihar Kogi don haka sun yarda cewa zai iya tabbatar da adalci ga kowa idan ya zama shugaban kasar Najeriya

Jihar Kogi - Fiye da malaman addinai na Kirista da musulunci sun taru a Abuja ranar Juma’a suna nuna goyon baya ga gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello don ya zama shugaban kasa a 2023, The Nation ta ruwaito.

Malaman sun ce Bello ne ya dace da ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2023 sakamakon ayyukan da suka gani ya yi a Jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Masu jini muke so: Gwamna ya caccaki tsofaffin da ke kwalamar kujerar Buhari

2023: Malaman addinin Musulunci da Kirista fiye 1,000 sun yi taron yi wa Yahaya Bello addu’o’in samun nasara
2023: Malaman addini musulunci da kirista fiye da 1,000 sun yi wa Yahaya Bello addu'ar samun nasarar zama shugaban kasa. Hoto: The Nation
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar su, Bello tsayayyen mutum ne wanda zai iya tabbatar da adalci ga ‘yan Najeriya idan ya zama shugaban kasa.

A cewarsu zaman Bello a matsayin magajin shugaba Buhari zai sa ‘yan Najeriya su kasance cikin kwanciyar hankali da hadin kai ba tare da bambancin addini ko yare ba.

Malaman addinai sun yaba da halayen Bello

Yayin jawabi kamar yadda The Nation ta ruwaito, Bishop Praise Moses ya ce Bello mutum ne mai son zaman lafiya wanda zai bunkasa kasar nan.

Moses ya ce Bello yana da ikon yaki da ta’addanci, batagarin ‘yan siyasa, ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran miyagun jama’a.

A cewar sa, sun yi taron ne don neman yardar Ubangiji akan zabar wa Najeriya shugaba na kwarai.

Bishop Moses ya ce:

“Ana yakinin da yardar Ubangiji, ta hanyar addu’o’i, Yahaya Adoza David Bello shi ne zai zama shugaban kasar Najeriya a zaben 2023 da za ayi."

Kara karanta wannan

Baki ya ke yanka wuya: An bukaci Tinubu ya bada hakurin abubuwan da ya fada tun 1997

Sheikh Abubakar ya bukaci jama’a su dinga addu’o’i da azumi don Bello ya samu nasara

Yayin jawabin Sheikh Abubakar ya ce Gwamnan Bello mutum ne mai gaskiya kuma jajirtacce wanda ake sa ran zai tallafa wa kasar nan ida Buhari ya sauka.

A cewar Abubakar, Bello zai samar da tsaro, zaman lafiya da kuma kaunar juna ga ‘yan Najeriya ba tare da bambancin addinai ko kabilu ba.

Don haka yace ya zama wajibi jama’a su zage wurin yin addu’o’i da azumi don gwamnan ya samu nasara inda yace gwamnan yana da duk wasu halaye da musulunci ya ke bukata a wurin shugaban na kwarai.

2023: Za mu bi didigin inda ƴan takara suke samo kuɗi, za mu sa ido kan asusun bankin ƴan siyasa, INEC

A wani rahoton kun ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, INEC, ta aika da muhimmin sako ga yan siyasa da jam'iyyun siyasa gabanin babban zaben shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Tanko Yakasai: 'Yan Arewa ba sa tsinana komai a Najeriya, a ba 'yan kudu mulki a 2023

Hukumar ta sha alwashin cewa za ta saka idanu a kan 'yan siyasa da jam'iyyun siyasa domin gano inda suke samo kudade domin yakin neman zabe, Vanguard ta ruwaito.

Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana hakan yayin wani taro da hukumar zaben ta shirya a Abuja, ranar Juma'a 21 ga watan Janairu, kuma ya ce hukumar za ta saka ido kan yadda aka hada-hadar kudade ranar zabe don dakile siyan kuri'u, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel