2023: Afegbua ya bar Atiku, ya ce ya shirya yaki da duk dan arewa da PDP ta bai wa takara

2023: Afegbua ya bar Atiku, ya ce ya shirya yaki da duk dan arewa da PDP ta bai wa takara

  • Tsohon mai magana da yawun kungiyar kamfen ta Atiku Abubakar, Kassim Afegbua, ya shawarci PDP da kada ta kuskura ta bai wa Atiku tikitin takara
  • A cewar Afegbua, Najeriya ta na bukatar matashi mai jini a jiki kuma dan Kudancin kasar nan, duba da rashin kwazon da Buhari ya nuna
  • Afegbua ya ce ya shirya yaki da duk dan arewa ko kuma tsohon da jam'iyyar adawar ta bai wa tikitin takara na shugabancin kasa 2023

Tsohon mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Atiku Abubakar a zaben 2019, Prince Kassim Afegbua, ya shawarci 'yan jam'iyyar PDP da su mika tikitin takarar shugabancin kasa na jam'iyyar zuwa kudu a maimakon bai wa Atiku saboda yawan shekarun sa.

A wata takarda da tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Edo ya fitar, ya ce kamata ya yi Atiku ya hakura da neman kujerar shugaban kasa kuma ya bai wa dan takarar kudu goyon baya domin tabbatar daidaito da adalci, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa zan nemi takarar kujerar Buhari a 2023 – Tsohon gwamnan Zamfara

2023: Tsohon kakakin Atiku ya waske, ya bayyana dan takarar da ya ke goyon baya
2023: Tsohon kakakin Atiku ya waske, ya bayyana dan takarar da ya ke goyon baya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce zai kasance mai suka tare da rashin gyon baya ga kowanne dan takarar arewa da ya nuna sha'awar zama shugaban kasa a zaben 2023 a cikin jam'iyyar PDP.

Ya shawarci kwamitin ayyukan kasa na jam'iyyar karkashin shugabancin Dr Iyorchia Ayu a su duba matashin dan takara, Daily Trust ta ruwaito.

Takardar ta ce:

"Ganin rashin kwazon da shugaban kasa Muhammadu Buhari nuna saboda shekarun sa, rashin dacewa da kuma rashin isa da gogewar siyasa wurin tsamo kaasar nan daga dukkan kalubale, akwai rashin dacewa a ce Alhaji Atiku Abubakar zai cigaba da nuna bukatarsa ta haye wa kujerar shugabancin kasar nan duk da yawan shekarun sa.
“Ba zai yuwu ya cigaba da zama dan takarar jam'iyyar nan ba a kowacce shekara sai ka ce shi aka kafa wa jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Shugabanci a 2023: 'Yan kamfen din Atiku sun yi watsi dashi sun kama wani dan takara

"Babu dabara ko kadan a ce tsohon ya na kokarin sake takara a wannan lokacin da halin da kasar nan ta ke ciki na bukatar matashin dan takara da kuma dan kudu".

Ya kara da cewa:

"Bayan zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar ya bar mu a Najeriya inda ya tafi Dubai neman mafaka, hakan yasa muka dinga fuskantar barazana da kalubale tare da hantara daga masu iko a jam'iyya mai mulki.
"Wannan tamkar Jana ne ya bar dakarun sa a filin daga. A maimakon ya dage sun samu kwarin guiwa daga wurin shi, rashin sa kuwa ya sa an fuskanci kalubale mai yawa. Ya na Dubai, ya bar mu bayau."

Asali: Legit.ng

Online view pixel