Da duminsa: Kashi 90 na gwamnonin Najeriya ba su da gogewar mulki, Hakeem Baba-Ahmed

Da duminsa: Kashi 90 na gwamnonin Najeriya ba su da gogewar mulki, Hakeem Baba-Ahmed

  • Mai magana da yawun NEF, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya ce kashi 90 cikin 100 na gwamnonin Najeriya basu san komai game da mulki ba
  • Ya ce an samu mutanen da ba su dace ba sun kwace mulki domin neman mulki ido rufe suke yi, hakan ya sa ba su kawo komai na ci gaba
  • Baba- Ahmed ya ce idan aka duba tsarin gwamnati kuma aka baje ta, sai a fara tambayar cewa me ce ce matsalar Najeriya?

Dr Hakeem Baba-Ahmed, mai magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), ya ce kashi casa'in cikin dari daga cikin gwamnonin Najeriya ko kusa ba su da alaka da mulki kafin su hau shi.

Yayin tattaunawa da Daily Trust a Abuja, Baba Ahmed ya ce abin da ya sa yayi imani da hakan shi ne ganowa da ya yi "basu da shiri, tushe da kuma gogewa a fannin mulki".

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi: Rashin tsaro shine matsalar kasar nan, shi yasa muka gagara ci gaba

Da duminsa: Kashi 90 na gwamnonin Najeriya ba su da gogewar mulki, Hakeem Baba-Ahmed
Da duminsa: Kashi 90 na gwamnonin Najeriya ba su da gogewar mulki, Hakeem Baba-Ahmed
Asali: Original
Ya ce "mun samu mutanen da ba su dace ba sun kwace mulki daga hannun mutane da suka dace da mulkin, haka ya sa ba su da kokarin kawo cigaban da ake bukata."
Sannan ya yi kira kan sake sabon tsarin kasar, inda ya ke cewa "abinda ya kamata mu yi shi ne mu duba tsarin mulkin tarayya sannan mu ce me ne ne matsalar?"
"Mene ne ya sa ba ya yuwuwa a rage mulki ko kuma a daidaita tsarin gwamnati, sake tsarin kasar? Wadannan kalamai masu matukar zafi ne ga mutane da yawa da ke mulki a yau."

Najeriya ba ta buƙatar shugaban ƙasa na ƙabilanci, Hakeem Baba-Ahmed

A wani labari na daban, Dr Hakeem Baba-Ahmed, mai magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewa ya ce Najeriya bata bukatar shugaban kasa na kabilanci, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rudani: Anata cece-kuce a Twitter yayin da mahaukaci ya yiwa wani kyautar kudi

Da ya ke jawabi wurin taron tattaunawa da Daily Trust ta shirya a Abuja, Baba-Ahmed ya koka kan yadda lamura ke kara zafafa a siyasan Najeriya gabanin babban zaben 2023.

A jawabin da ya yi game da wahalhalun da ake fama da shi a kasar, Baba-Ahmed ya ce:

"Daya daga cikin abubuwa mafi muni da za ka iya yi domin kara fusata mutane kan matsalin rayuwa shine, kara kudin man fetur, farashin kayayaki, hakan na jefa mutane cikin tsananin damuwa kuma kana son yin zabe nan da wasu watanni?"

Asali: Legit.ng

Online view pixel