Wadanda Tinubu ya ba mukamai a shekarun baya, sun dawo za su taya shi yakin 2023

Wadanda Tinubu ya ba mukamai a shekarun baya, sun dawo za su taya shi yakin 2023

  • Wasu shugabannin kananan hukumomi da aka yi a jihar Legas su na tare da Bola Tinubu a 2023
  • ‘Yan kungiyar Grassroots Network for Asiwaju Bola Tinubu sun fara yi wa tsohon mai gidansu kamfe
  • Shugaban GNAT, Abiodun Mafe, ya ce Tinubu ne wanda ya yi masu riga da wando a tafiyar siyasa

Lagos - A ranar 19 ga watan Junairu, 2022 aka ji tsofaffin shugabannin kananan hukumomi na jihar Legas sun fara yi wa Asiwaju Bola Tinubu kamfe.

Wasu daga cikin tsofaffin shugabannin kananan hukumomin da ke karkashin Grassroots Network for Asiwaju Bola Tinubu sun fara shirin takara.

‘Yan kungiyar ta GNAT sun bayyana cewa ba za su juyawa uban gidansu da ya taimaka masu a siyasa baya ba. Daily Trust ce ta fitar da wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Tseren shugabancin APC ya koma tsakanin Sanatoci 2, da tsohon Ministan Buhari

A cewar ‘Yan tafiyar Grassroots Network for Asiwaju Bola Tinubu, gwaninsu ne ya fito da wasu daga cikin manyan ‘yan siyasar da ake jin labarinsu a yau.

GNAT tace daga cikin mutanen da Bola Tinubu ya yi wa horo akwai Lai Mohammed, Rauf Aregbesola, Babatunde Fashola, da ma wasu ire-irensu.

'Yan Tinubu
Kungiyoyin Magoya bayan Bola Tinubu Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Su wanene GNAT?

GNAT kungiya ce mai kunshe da tsofaffin shugabannin kananan hukumomi, kansiloli, sakatarorin shugabannin kananan hukumomi da hadimai.

Kamar yadda jaridar ta fitar da rahoto, kungiyar siyasar ta kunshi duk sauran wadanda suka rike mukamai a matakin karamar hukuma a gwamnatin Legas.

Shugaban wannan tafiya, Abiodun Mafe, ya ce ba za su yi butulci, su manta da abin da tsohon gwamnan ya yi masu har suka kai inda suka kai a siyasa ba.

Tinubu ya baza yara

A halin yanzu Lai Mohammed shi ne Ministan yada labarai da al’adu. Lai yana cikin manyan hadiman Tinubu a lokacin da yake gwamnan jihar Legas.

Kara karanta wannan

Alamar tambaya: Garba Shehu ya lallaba ya bibiyi shafin kamfen din Tinubu a Twitter

Babatunde Fashola wanda yanzu yake rike da Ministan ayyuka da gidaje, ya taba zama shugaban ma’aikatan fadar gidan gwamnati a lokacin mulkin Tinubu.

Bayan Tinubu ya yi shekara takwas a mulki, Raji Babatunde Fashola ne ya karbi ragamar Legas.

A 1999 Tinubu ya nada Rauf Aregbesola a matsayin kwamishinansa na ayyuka. Daga baya ya zama gwamna a jihar Osun, kafin yanzu a nada shi Minista.

Tinubu ya yi kata-bora

Jiya Bola Tinubu ya nemi mutane su yafe tuntuben bakinsa, ya kuma yi kira na musamman ga mata bayan INEC tayi masa raddi na cewa PVC sun tashi aiki.

Mai magana da yawun bakin jagoran APC, Tunde Rahman ya fitar da jawabi, yana bayyana inda Mai gidan na sa ya yi subul-da-baka da yake jawabi a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel