Alamar tambaya: Garba Shehu ya lallaba ya bibiyi shafin kamfen din Tinubu a Twitter
- Hadimin shugaban kasa kan harkokin labarai, Garba Shehu, ya bibiyi shafin magoya bayan Tinubu a Twitter
- Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta dage takunkumin da ta sanyawa dandamalin
- Shehu na daya daga cikin hadiman Buhari da suka fara wallafa rubutu a shafin bayan ta fara aiki
Babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin labarai, Garba Shehu, na bibiyar shafin magoya bayan babban jigon APC, Bola Tinubu wato ‘Tinubu Media Support Group’ a twitter.
Shehu na daya daga cikin hadiman shugaban kasa na farko da suka fara wallafa a twitter tun bayan da aka dage haramcin da aka sanya ma dandamalin a ranar 13 ga watan Janairu, kuma tun lokaci yake amfani da ita sosai.
Jaridar Punch ta rahoto cewa kafin haramcin, Shehu wanda ya fara Twitter a watan Afrilun 2015 yana bibiyar shafuka 365.
Sai dai kuma, adadin wadanda yake bibiya ya karu zuwa 366; inda masu amfani da dandalin sama da miliyan 1.2 ke bibiyar nasa shafin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An lura cewa shafin da ya bi a baya-bayan nan shine na kamfen din Tinubu. Sannan ana ganin hakan zai dasa ayar tambaya kan ko shima yana tare da jigon na jam'iyyar mai mulki.
Jaridar The Nation ta kuma rahoto cewa an bude shafin ‘Tinubu Media Support Group (TMS), @TinubuMediaS’ ne a watan Janairu bayan tsohon gwamnan na jihar Lagas y ace zai tsaya takarar tikitin shugaban kasa na APC.
A farkon watan nan ne dai tsohon gwamnan na jihar Lagas ya bayyana aniyarsa na son tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Bola Tinubu ya bayyana babban abinda zai fara yi wa Talakawan Najeriya bayan zama shugaban ƙasa a 2023
A gefe guda, jagoran jam'iyyar APC na ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya fara bayyana wa yan Najeriya manufofinsa bayan ɗarewa karagar mulki a 2023.
A wani bidiyo da jaridar Punch ta sanya a shafinta na Facebook, Tinubu, ya ce, gwamnatinsa zata maida jarabawar WAEC kyauta ga yan Najeriya.
A cewarsa, da zaran ya ɗare karagar mulki a 2023, yan Najeriya sun gama kuka kan biyan kuɗin WAEC, zai biya wa kowane ɗalibi a Najeriya.
Asali: Legit.ng