Zaben 2023: Hadimin Buhari ya bayyana adawarsa ga tsayawar Tinubu takarar shugaban kasa

Zaben 2023: Hadimin Buhari ya bayyana adawarsa ga tsayawar Tinubu takarar shugaban kasa

  • Hadimin Muhammadu Buhari kan harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu, ya bayyana matsayarsa a kan takarar babban jigon APC, Bola Tinubu
  • Kai tsaye Ojudu ya bayyana adawarsa da tsayawar Tinubu takarar shugaban kasa a zaben 2023
  • Ya kuma bayyana cewar kada wanda ya kirasa da maciyin amana don kawai ya bi ra'ayin kansa

FCT, Abuja - Mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kan harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu, ya bayyana adawarsa ga takarar babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, wanda ke neman takarar shugaban kasa a 2023.

Tun bayan da Tinubu ya ayyana aniyarsa na takarar shugaban kasa, ana ta samun martani mabanbanta a kan lamarin.

Yayin da wasu ke nuna goyon bayansu ga Tinubu, wasu mutane ciki harda masu yi masa biyayya sun sha alwashin yin adawa da shi. Daga cikinsu harda hadimin shugaban kasar (Ojudu).

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu

Zaben 2023: Hadimin Buhari ya bayyana adawarsa ga tsayawar Tinubu takarar shugaban kasa
Zaben 2023: Hadimin Buhari ya bayyana adawarsa ga tsayawar Tinubu takarar shugaban kasa Hoto: @AsiwajuTinubu, @babaloveme3
Asali: Twitter

A cikin wata sanarwa da ya saki a shafinsa na Facebook a ranar Talata, 18 ga watan Janairu, Ojudu ya yi watsi da batun cewa duk wani na kusa da Tinubu da ke adawa da takararsa na shugaban kasa maciyin amana ce.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hadimin shugaban kasar ya tabbatar da cewar har yanzu Tinubu na a matsayin jagoransa kuma zai ci gaba da girmama shi da irin gudunmawar da ya ba kungiyarsa a lokacin yaki da sojoji.

Sanarwar ta ce:

"Na ga wani jawabi da nayi shekaru da dama da suka gabata don murnar cikar Sanata Bola Ahmed Tinubu shekara 60 da haihuwa yana yawo. Eh ni nayi wannan jawabi. Kuma irin haka da dama na nan zuwa a cikin tarihin rayuwata. Mu, tare, mun ga ranaku masu kyau da ranaku marasa kyau.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa na yarda zan lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Tinubu

"Ni da Bola Tinubu mun yi nisa a rayuwa kuma mun tsayawa juna. Don haka, kada wanda yayi amfani da jawabina na kyawawan ayyukansa da kuma kin mara masa baya da nayi a kudirinsa na neman shugabancin Najeriya wajen kakaba mani sunan maciyin amana.
"Tinubu na nan a matsayinsa na jagorana kuma zan ci gaba da girmama shi har abada da kuma gudunmawar da ya bawa kungiyata a lokacin yakinmu da soji.
"Sai dai shi ya san cewa ni ba dan abi yarima a sha kida bane. Ina bin zabina ne. Zai gaya muku ni mai zaman kansa ne a ayyuka da hanyoyina.
"A matsayin dalibin jami'a da ke mataki na uku mahaifina ya zabi kasancewa a NPN. Ban taba duba wai cewa shi ke ciyar dani da biya mun kudin makaranta ba wajen bin sa jam'iyyar da bana ra'ayi. Na je UPN kuma na zama shugaban matasa.
"Tinubu zai fada maku duk wani abu da kuma duk wanda Ojudu ya kuduri aniyar kasancewa tare da shi toh zai kasance dari bisa dari. Dalilan da suka sa na gwammaci na fuskanci azabtarwa da yiwuwar mutuwa a tsareni da Janar Sani Abacha yayi da in bayyana wasu abubuwa da suke so in bayyana game da shi.

Kara karanta wannan

Fitaccen dan jarida, Dele Momodu ya ayyana kudurin tsayawa takara a 2023 a PDP

"Mun riga mun ginu kafin muka hadu da shi kuma a cikin tarayyarmu mun taimaki junanmu. Tun a shekarar 1992 da na san shi na riga na kasance daya daga cikin editocin wata shahararriyar mujallar labarai da nagarta sosai a cikin al’umma. Na bar aikina ne a lokacin da hamshakin attajirinmawallafin nan namu (Cif MKO Abiola) ya bukaci ni da abokan aikina da mu nemi afuwar Janar Ibrahim Babangida kan wani labari na sukar gwamnatin. Wannan ya kasance a 1992.
"Da na bar wannan aikin, Cif Gani Fawehinmi, mutumin da nake ganin mutunci sosai (ya bani tallafin karatu a lokacin da nake makaranta tare da King Sunny Ade) ya zuba jari a dandamalin wallafa na (The News, mawallafin PM news). Kuma wanda ya taka rawar gani a yaki da dawowar damokradiyya Najeriya.
"A karshen wannan gwagwarmaya, Cif Fawehinmi ya ce lallai sai mun bar siyasa. Sanata Bola Ahmed Tinubu ya ki yarda da wannan ra'ayin, nima kuma na bi. Cike da rufewar ido don yin biyayya, na bi Sanata Tinubu harma na taka rawar gani a wasu muhimman lamura a lokacin da ya kama mukamin gwamna. Abun da nayi ya fusata Cif Gani sosai da har sai da ya nemi na biya jarinsa da ya zuwa. Kun san me? na yi hakan cike da farin ciki.

Kara karanta wannan

2023: Na manta ban sanar da Buhari zan yi takarar shugaban kasa ba - Tsohon mataimakin gwamnan CBN

"Don haka idan ra'ayin rikauna ya yi aiki kan NPN, kan IBB da kan "zauna ka kalla" bai zamo cin amanar mahaifina, Cif MKO Abiola da Cif Gani Fawehinmi ba, toh ta yaya ra'ayin rikauna zai zama hakan ga kudirin shugabanmu na yanzu?
“Don haka, a kan wannan al’amari na 2023 ina yi masa fatan alheri amma ba zan iya ba shi goyon baya ko jefa masa kuri’a a zaben fidda gwanin da ke tafe ba. Hakkina ne. Na haura shekaru 60 don Allah. Na kusan mutuwa ina neman wannan hakkin dimokradiyya da ba za a iya tauyewa ba, wanda aka tsare kuma aka azabtar. Ubangijinku ba ubangijina ba ne.”

Hadimin Shugaban kasa ya bayyana inda aka kwana game da batun ‘takarar’ Osinbajo

A wani labarin, mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa, Babafemi Ojudu ya tanka masu rade-radin cewa Yemi Osinbajo zai yi takara.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Na shirya yin gaba da gaba da Tinubu a zaben fidda gwanin APC – Shahararren sanata

Tun tuni ake ta jita-jitar cewa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo zai nemi tikitin takarar shugaban Najeriya a jam’iyyar APC a 2023.

Da yake bayani a shafinsa na Facebook, Babafemi Ojudu yace ‘yan siyasa da-dama su na ta zuwa ofishinsa domin jin ko Osinbajon zai tsaya takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel