APC za ta kasa kujeru, a cire Yari, Modu Sheriff daga cikin masu neman Shugaban jam’iyya

APC za ta kasa kujeru, a cire Yari, Modu Sheriff daga cikin masu neman Shugaban jam’iyya

  • A watan gobe za a san su wanene sababbin shugabannin jam’iyyar APC mai mulki na kasa a Najeriya
  • Shugabannin rikon kwarya na APC sun fara tattaunawa a kan yadda za a yi kason mukamai a NWC
  • Da alamu ba za a kai kujerar shugaban jam’iyya zuwa Arewa maso gabas ko kuma Arewa ta yamma ba

Abuja - Da alamu shugabannin jam’iyyar APC sun zabi duk wanda zai zama sabon shugaban jam’iyya na kasa ya fito daga bangaren Arewa maso tsakiya.

Wani rahoto da Punch ta fitar a ranar Laraba, 19 ga watan Junairu, 2022 ya bayyana wannan.

Wani babba a tafiyar APC, ya shaidawa jaridar cewa yankin Arewa ta tsakiya za a kai kujerar shugaban jam’iyya, sai a ba yankin Kudu maso gabas sakatare.

Kara karanta wannan

Masu jini a jika: 'Yar shekara 38 ta ce ba wanda ya dace ya gaji Buhari sai ita a 2023

Majiyar ta ce kujerar mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kudancin Najeriya za ta fito ne daga yankin kudu maso kudancin kasar nan a zaben da za a gudanar.

Kujerun da suke hannun ‘yan siyasar Arewa za su koma wajen takwarorinsa a kudu. Haka zalika za a iya musayar mukaman da ‘yan kudu suka rike kafin yanzu.

Shugaban APC
Shugaban APC na riko, Mai Mala Buni Hoto: Kashim Mustapha Yusufari
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Kawo yanzu mun yarda cewa Arewa maso tsakiya ta samu kujerar shugaban jam’iyya, sai kudu maso kudu ta samu mataimakin shugaba na shiyyar kudu.”
“Kudu maso gabas za su samu mukamin sakataren jam’iyya. Mukaman da ‘Yan Arewa suka rike a NWC za su je ‘Yan kudu. Amma kowa na iya yin takara.”

- Wani babba a APC.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, duk da wannan mataki da kwamitin CECPC za a dauka, ba zai hana masu sha’awar neman wata kujera su tsaya takara ba.

Kara karanta wannan

Atiku, Kwankwaso sun tsaya wasa, ‘Yan siyasa 2 sun bayyana niyyar tsayawa takara a PDP

Lissafi zai canza

Idan aka tafi a haka, masu neman kujerar shugaban jam’iyyar APC na kasa daga Arewa maso gabas da Arewa maso yammacin Najeriya ba za su kai labari ba.

Daga cikin wadanda za su fito daga wannan rukuni akwai tsofaffin gwamnoni irinsu; Abdulaziz Yari, Ali Modu Sheriff, Isa Yuguda da Sunny Sylvester Moniedafe.

Su wa za su taki sa'a?

A baya kun ji cewa masu neman cin gadon Mai Mala Buni sun hada da wasu Ministoci da kuma Sanatoci masu-ci daga yankin Arewa maso tsakiyar Najeriya.

‘Yan kan gaba su ne Sanata mai wakiltar jihar Neja ta gabas, Mohammed Sani Musa da Tanko Al Makura mai wakiltar Nasarawa ta kudu, sai su George Akume.

Asali: Legit.ng

Online view pixel