Abin da ya sa ake bukatar a gyara dokar zabe kafin 2023 inji Tsohon Shugaban INEC, Jega

Abin da ya sa ake bukatar a gyara dokar zabe kafin 2023 inji Tsohon Shugaban INEC, Jega

  • Farfesa Attahiru Jega ya bada shawarar a gyara dokar zabe na kasa kafin a shirya zabe mai zuwa
  • Jega ya na ganin akwai wasu abubuwan alheri a kudirin zaben da shugaban kasa ya yi watsi da shi
  • Tsohon shugaban hukumar zabe na Najeriya ya bayyana kuskuren ‘yan majalisa da yadda za a gyara

Abuja - Farfesa Attahiru Jega, tsohon shugaban hukumar INEC ya ce akwai bukatar ayi zabe mai zuwa da sabon dokar zabe. Daily Trust ta fitar da wannan rahoto.

Da yake magana jiya a wajen wani zama da kungiyar YIAGA ta shirya da mutane a Abuja, Attahiru Jega ya ce shirya zabe mai nagarta yana da wahala sosai.

A ra’ayin Farfesa Jega, akwai abubuwan tambaya a tattare da kudirin zaben da shugaba Muhammadu Buhari ya ki sa hannu, amma akwai wasu alheri a ciki.

Kara karanta wannan

Zaman lafiya ya samu: Gwamna Buni ya yabawa Buhari bisa magance rashin tsaro a Arewa

Attahiru Jega ba ya goyon bayan ayi watsi da kudirin kaco-kam dinsa saboda kura-kuren da ke ciki.

“Ina ganin ya kamata Najeriya ta yi zabe mai zuwa da sabuwar doka domin akwai abubuwa da-dama a kudirin zaben da za su gyara zabukanmu.”
“Kamar yadda na fada a baya, tun shekarar 2010, ba a samu wani gagarumin cigaba a kan harkar dokar zabe a kasar nan ba.” – Farfesa Attahiru Jega.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon Shugaban INEC
Muhammadu Buhari da Farfesa Attahiru Jega Hoto: saharareporters.com
Asali: UGC

Inda Majalisa tayi kuskure

A matsayin shawara, Jega ya ce bai kamata ‘yan majalisa su nemi su shigo da dokar da karfi da yaji ba, ya ce majalisar ta kawo kudirin ne ba tare da duba da kyau ba.

Farfesan ya so a ce ‘yan majalisa sun yi la’akari da wasu abubuwa a doka kafin a shigo da kudirin.

Zaben tsaida gwani

Kara karanta wannan

Umahi ga 'yan Najeriya: Bai kamata kuke tsoron inyamuri ya zama shugaban kasa a 2023 ba

Jaridar Punch ta kuma rahoto Jega yana magana a game da muhawarar da ake yi a kan yunkurin wajabtawa jam’iyyu amfani da ‘yar tinke wajen zaben tsaida gwani.

Jega yake cewa duk gwamnan da zai iya murde zaben da ake amfani da wakilan jam’iyya wajen fito da ‘dan takara, haka zalika zai iya tafka magudi a zaben ‘yar tinke.

“A ba hukumar INEC dokar domin ta fara shiryawa zaben 2023. Abin da mu ke cewa shi ne bai kamata a jefar da jariri tare da ruwan wankan gaba daya ba."
“A duba abubuwan alheri a cikin kudirin, a sa hannu ya zama doka ba tare da wani bata lokaci ba, saboda INEC ta fara shiryawa zaben 2023 da kyau.”

Siyasar 2023

A makon da ya gabata ne mu ka ji babban jigon APC a kudu maso yammacin Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya fara gyara dangantakar da ke tsakaninsa da abokan fadansa.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Shehu Sani ya bayyana matsayinsa a kan tsarin mulkin karba-karba

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi wani zama da Kayode Fayemi a kan yadda za a bullowa 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel