Matakan da PDP zata bi wajen fitar da dan takarar shugaban ƙasa a 2023, Gwamna ya magantu

Matakan da PDP zata bi wajen fitar da dan takarar shugaban ƙasa a 2023, Gwamna ya magantu

  • Gwamna Wike na jihar Ribas yace jam'iyyar APC ba zata yi gaggawar aiwatar da tsarin karba-karba wajen fidda dan takara a 2023
  • Wike yace wajibi PDP ta zauna ta yi nazari kan abin da yan Najeriya ke so, sannan ta duba wanda zai iya nasara a zaɓe
  • Allah ba zai yafe wa jam'iyyar PDP ba matukar ba ta lashe zaɓe ba kuma ba ta ceto Najeriya daga bakin mulkin APC ba, inji Wike

Oyo - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yace jam'iyyarsa ta PDP zata duba muradin yan Najeriya da kuma wanda zai iya lashe zabe wajen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023.

Tribune Online ta rahoto cewa gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da ya jagoranci jiga-jigan PDP suka kai wa gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ziyara a gidan gwamnati dake Ibadan.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta bayyana shugabannin da take zargin suna taimakawa yan bindiga a Najeriya

Wike yace PDP ta gano cewa yan Najeriya ba zasu ji daɗi ba matukar ta fitar da ɗan takarar da ba shi da kwarjinin samun nasara a zabe.

Gwamna Nyesom Wike
Matakan da PDP zata bi wajen fitar da dan takarar shugaban ƙasa a 2023, Gwamna ya magantu Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yace ya zama wajibi mambobin PDP su natsu su fitar da ɗan takaran da zai iya lashe zabe, domin ceto Najeriya daga, "Sheɗaniyar gwamnatin APC."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda PDP zata fidda dan takara

A jawabinsa, gwamna Wike yace:

"Kowa yasan cewa a kan maganar kujerar shugaban ƙasa muna da ra'ayoyi mabanbanta. Amma daga karshe PDP zata zauna ta duba yanayin yan Najeriya, da abin da suke so."
"Ta kowane hanya zamu zauna mu ɗauki matakin da zai faranta ran ƴan Najeriya, kuma wanda zai ba mu nasara a zaɓe."
"Ba zan iya cewa ina goyon bayan masu kiran akai tikiti yankin Kudu ba, duk da mun riga mun yanke hukunci, amma hakan ba zai sa mu yi watsi da yan uwan mu na sauran sassan ƙasa ba."

Kara karanta wannan

2023: Ƴan Najeriya na son PDP ta karɓi shugabancin ƙasa daga hannun APC, Wike

Allah ba zai yafe ma PDP ba - Wike

Wike ya ƙara da cewa yana da yakinin daga ƙarshe jam'iyyar PDP zata ɗauki matakin da zai ɗaga martabar jam'iyyar.

"Bai dace yan Najeriya su cigaba da fama da wannan yanayin ba, Allah ba zai yafe wa PDP ba matukar ba ta cece Najeriya ba."
"Saboda idan muka sake rashin nasara a wannan lokacin, tabbas yan Najeriya ba zasu ji dadi ba. Ba zamu bar yanayin nan ya dore ba."

A wani labarin kuma Bayan sanar da shugaba Buhari, Gwamnan APC ya bayyana dalilin da yasa zaiyi gogayya da Tinubu a 2023

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, yace kusancinsa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yasa yake son dora wa daga inda ya tsaya.

Gwamnan yace dumbin ayyukan da ya yi wa mutanen jiharsa kaɗai sun isa ya nemi takara a 2023 domin kwatanta haka a ƙasa.

Kara karanta wannan

Tsarin karba-karba: Jam'iyyar PDP ta magantu kan wanda zata baiwa takarar shugaban ƙasa a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel