Hadimin Buhari ya fara lale maraba da dawowar tsohon Gwamna Kwankwaso Jam’iyyar APC

Hadimin Buhari ya fara lale maraba da dawowar tsohon Gwamna Kwankwaso Jam’iyyar APC

  • Hadimin Shugaban Najeriya ya taya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso murnar dawowa Jam’iyyar APC
  • Sanata Babafemi Ojudu yace bai tabbata da rade-radin da suke yawo cewa Kwankwaso ya bar PDP ba
  • Mai magana da yawun tafiyar Kwankwasiyya, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya karyata jita-jitar da ake yi

FCT, Abuja - Babafemi Ojudu, mai taimakawa shugaban kasa da shawarwarin siyasa ya yi magana a kan rade-radin dawowar Rabiu Musa Kwankwaso APC.

Sanata Babafemi Ojudu ya nuna farin cikinsa game da rade-radin da ke yawo cewa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso zai dawo jam’iyya mai mulki.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a shafinsa na Facebook dazu, Hadimin shugaban kasar ya bayyana Sanata Kwankwaso da gawurtaccen ‘dan siyasa mai jama’a.

A cewar Babafemi Ojudu, shigowar Kwankwaso jam'iyyar APC, za ta taimaka masu sosai.

Gwamna da Kwankwaso
Ana cewa Kwankwaso zai koma APC Hoto: @mohd.saifullahi.9
Asali: Facebook

Maganar da Babafemi Ojudu ya yi a Facebook

“Labari ya karada ko ina cewa jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwakwanso, ya dawo jam’iyyarmu ta APC.”
“Ban tabbatar da wannan labarin ba tukuna, amma idan har gaskiya ne, mu na matukar yi masa murna.”
“Wannan zai kasance mafi kyawun dabarar da zai yi a siyasarsa. Mai jama’a, kwararren mai hada taro, kuma rikakken ‘dan siyasa.”
“Kwankwaso shi ne jagoran masu jar hula. Shigowansa zai taimaka mana sosai a tafiyarmu na kawo gyara a Najeriya.”

- Babafemi Ojudu

Da jaridar Daily Trust ta tuntubi kakakin cibiyar yada labarai na Kwankwasiyya, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya musanya labarin jita-jitar jagoran na su.

Malam Sunusi Bature Dawakin Tofa yace rade-radin ba gaskiya ba ne, kuma basu da wani tushe.

A wata doguwar hira da tsohon Ministan tsaron ya yi da jaridar Punch, babu inda ya bayyana cewa ya na da niyyar barin PDP, ya koma APC da ake ta rade-radi.

Kwankwasiyya ta kama 'Dan Buhariyya

Kwanaki aka ji wani mai amfani da Facebook, Sirajo Saidu Sokoto ya bayyana cewa ya daina goyon bayan Muhammadu Buhari, ya shiga tsagin Kwankwasiyya.

Dalilin wannan mutumi na yin haka shi ne, an yi garkuwa da ‘yanuwansa biyar kuma babu wanda ya taimaka masa har suka biya 'yan bindiga kudin fansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel