Babban hadimin tsohon Gwamna Okorocha ya karyata zargin wata alaka da ‘Yan bindiga

Babban hadimin tsohon Gwamna Okorocha ya karyata zargin wata alaka da ‘Yan bindiga

  • Uche Nwosu yace abin da ya sa ‘Yan Sanda suka kama sa shi shine zargin ya na taimakawa ‘yan ta’adda
  • Nwosu yace babu abin da ya hada shi da ‘yan bindiga kamar yadda aka sanar da jami’an ‘yan sanda
  • ‘Dan takarar gwamnan ya na so ayi bincike domin a gano wanda ya mallaki jirgin da aka kai shi Abuja

Imo - Tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Imo a lokacin Rochas Okorocha, watau Mista Uche Nwosu yace ana zarginsa da laifin ta’addanci.

A wani rahoto da Vanguard ta fitar, Uche Nwosu ya bayyana cewa an rubuta korafi a kansa zuwa ga ‘yan sanda, ana tuhumarsa da taimakawa ‘yan ta’adda.

Da yake bayanin halin da ya shiga bayan an kama shi, Nwosu yace jami’an ‘yan sanda sun shaida masa cewa wani ya rubuto takarda, ya na tuhumarsa da laifi.

Kara karanta wannan

Yadda ɗan gani kashenin Buhari ya koma Kwankwasiyya bayan ƴan bindiga sun sace ƴan uwansa 5

Kamar yadda ya yi bayani, surukin na tsohon gwamna Rochas Okorocha yace ana zarginsa da taimakawa ‘yan bindiga da makamai, da kuma ba su kudi.

‘Dan siyasar yace ba a taba kiran shi domin ya amsa tambayoyi a kan zargin da ake yi masa ba.

Hadimin tsohon Gwamna Okorocha
Uche Nwosu a tsare Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

The Nation ta rahoto Nwosu ya na yin kira ga Sufetan ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya binciki wanda ya mallaki jirgin saman da aka kai shi Abuja a cikinsa.

Abin da Uche Nwosu ya fadawa 'yan jarida

“An ce korafin da aka kai wa ‘yan sanda ya fito daga wajen wani ne, dalilin kama ni shi ne ina taimakawa ‘yan bindiga da makamai da kudi.”
“A cikin gidan gwamnatin Imo aka kitsa wannan sharri. Jami’an tsaron gidan gwamnati, da wani mai suna Shaba ne suke da hannu a wannan aiki.”

Kara karanta wannan

Yadda masu rike da madafan iko suka taka mai tsaron Buhari a Aso Villa da gidan 'Yan Sanda

“An yi wannan ne domin a ci mani mutunci, a bata mani suna. Babu wani jami’in tsaro da ya zo daga Abuja da ya zo ayi wannan aikin da shi.” - Nwosu

Nwosu ya yi tir da jami’an da suka shigo cikin coci domin su yi gaba da shi a lokacin da mutane suke ibada, a maimakon a gayyace shi domin ya wanke kansa.

Maganar Manjo Hamza Al-Mustapha

Tsohon Dogarin Janar Sani Abacha ya jefi manyan masu kudin Najeriya, da wadanda aka ba damar hako ma’adanai da zargin tada zaune-tsaye a kasar nan.

Manjo Hamza Al-Mustapha yace sai an yi da gaske kafin a iya magance halin da Najeriya ta ke ciki saboda masu kudi su na kashe kudinsu domin tada tarzoma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel