Kwankwaso ya bayar da auren diyar Sanata Shekarau a Kano

Kwankwaso ya bayar da auren diyar Sanata Shekarau a Kano

  • Mutane da dama sun niki gari don zuwa daurin auren diyar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau
  • Kwankwaso ne ya zama waliyyi wanda ya bayar da auren diyar tsohon gwamnan, Halima Ibrahim Shekarau (Amira) ga Adamu Yusuf Maitama
  • An yi daurin auren ne a masallacin Umar Bn Khattaba da ke kan titin Zaria kuma manyan mutane kamar shugaban majalisar dattawa sun halarta

Kano - Mutane da dama sun samu damar halartar daurin auren diyar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, Daily Trust ta ruwaito.

Kwankwaso ne ya zama Waliyyi wanda ya bayar da auren diyar tsohon gwamnan, Halima Ibrahim Shekarau (Amira), ga Adamu Yusuf Maitama.

Kwankwaso ya bayar da auren diyar Sanata Shekarau a Kano
Kwankwaso ya bayar da auren diyar Sanata Shekarau a Kano. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito yadda aka yi daurin auren a masallacin Umar Bn Khattab da ke kan titin Zaria inda manyan mutane kamar shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, Sanata Barau Jibrin da manyan ‘yan siyasa.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano ta rikide, a yau Kwankwaso zai aurar da ‘Diyar cikin abokin adawarsa, Shekarau

Daruruwan masoya daga jam’iyyun biyu sun je bikin yayin da kowannensu ya je don nuna kauna ga shugabansa musamman mutanen Kwankwaso da suka isa wurin da jajayen huluna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da Kwankwaso ya nufi gidansa, Shekarau ya tafi nasa gidan tare da shugaban majalisar dattawan wanda daga baya suka bi Kwankwaso har gidansa don yi masa ta’aziyyar kaninsa da ya rasu.

Dama Shekarau ya je gidan Kwankwaso yi masa ta’aziyya a ranar Alhamis.

Shekarau da Kwankwaso su ne manya ‘yan siyasa masu mabiya da dama ba a Kano kadai ba har a Najeriya.

Kotu ta tabbatar da tsagin Shekarau matsayin sahihan shugabannin APC a Kano

A wani labari na daban, wata babbar kotun tarayya dak zamanta a birnin tarayya Abuja karkashin jagorancin Mai Sharia Hamza Muazu ta tabbatar da tsagin Shekarau ta gudanar da zaben shugabannin jam'iyyar APC a Kano.

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnoni 6 suka hana Majalisa juyawa Shugaban kasa baya a kan kudirin gyara zabe

Yayin Shari'a ranar Juma'a, Alkalin ya yi watsi da karar tsagin Ganduje kuma ya ci su tarar milyan daya kan batawa kotu lokaci, rahoton DailyNigerian.

Kotu ta tabbatar da cewa zaben da tsagin Shekarau tayi shine daidai kuma shugabanninsu ne shugabannin APC a jihar.

Abdullahi Abbas ne ke jagorantar tsagin Ganduje yayin da Ahmadu Haruna Zago ke jagorantar tsagin Shekarau.

A baya zaku tuna cewa a ranar 30 ga Nuwamba, kotu ta soke dukkan shugabannin jam'iyyar All Nigeria Peoples Congress da ke biyayya ga Gwamna Abdullahi Ganduje.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel