Manyan jiga-jigan PDP da daruruwan mambobi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki

Manyan jiga-jigan PDP da daruruwan mambobi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki

  • Wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP da magoya bayansu sun sauya sheka zuwa APC a jihar Cross River
  • Gwamnan jihar Ben Ayade, yace babu kowa a jam'iyyar PDP ta jihar, tsagin adawa ya mutu murus
  • Gwamnan ya kuma tabbatar wa mutanen jiharsa cewa za'a cigaba daga inda aka tsaya kan mulkin karba-karba da aka fara tun 1999

Cross River - Jiga-jigan PDP tare da dandazon magoya bayansu daga mazaɓar sanata ta kudancin jihar Cross Ribas sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC ranar Alhamis.

Da yake jawabi a wurin taron karɓan masu suaya sheka, Gwamna Ben Ayade na jihar Cross Riba, yace maganar tsarin mulkin karba-karba da aka fara a jihar tun 1999 yana nan daram.

Punch ta ruwaito cewa matukar aka cigaba da tsarin, yankin kudancin jihar ne zai fitar da gwamna na gaba a shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ba zai iya magance matsalar tsaro a shekara mai zuwa ba, inji minista

Ben Ayade
Manyan jiga-jigan PDP da daruruwan mambobi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ayade ya misalta PDP da wata jam'iyyar da ta tafka asara, ya kuma kara da cewa ya zama wajibi a kansa ya tabbatar cewa al'ummarsa sun guje ta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Vanguard ta rahoto Gwamnan yace:

"Ba halina bane ba, zan cika akawari. Shekarar 2023 lokaci ne na zaman lafiya, daidaito da adalci saboda kowa yasan ana yi da shi, kuma mu rinka baiwa kowa hakkinsa a siyasa."
"Wannan zai baiwa kowa dama yasan an zo kansa a lokacin da ya dace. Idan na duba tarihin Cross Ribas ina mamakin daga ina tsagin hamayya ke fitowa."
"Jam'iyyar PDP ta mutu, babu komai a cikinta. Jam'iyyar APC ce ke jan ragama yanzu, duk mai son cigaba da ganin mu a bangaren adawa to ba ya mana fatan alheri."

Gwamnan ya kuma bayyana cewa jam'iyyar APC ta samu gurin zama a jihar Cross Ribas, kuma an samu banbanci tsakanin lokacin baya da kuma yanzu.

Kara karanta wannan

Yanzu kam lokaci ya yi da ya kamata kowa ya nemi makami, gwamna Masari ya magantu

"Waɗan da suka gina PDP kuma suke tafiyar da ita, sune ke dawo wa cikin mu a APC yau. Me kuma ya yi saura a PDP ta Cross Ribas? ta mutu kawai."

A wani labarin na daban kuma Tsohon gwamnan Kaduna, Ramalan Yero, Ya bayyana shirinsa na tsayawa takara a zaben 2023

Tsohon gwamnan Kaduna, Ramalan Yero, yace a halin yanzun wuƙa da nama na hannun mutane su tantance tsakanin PDP da APC.

Yero, wanda ya sha kaye a hannun El-Rufai a 2015, yace mutane sun gwada PDP na shekara 16, sun kuma gwada APC na shekara 8.

Asali: Legit.ng

Online view pixel