Ka yi alkawarin zaben Tinubu matsayin mataimakinka amma ka saba: Akande ga Buhari

Ka yi alkawarin zaben Tinubu matsayin mataimakinka amma ka saba: Akande ga Buhari

  • Tsohon shugaban APC, Bisi Akande, ya bayyana wasu abubuwan da suka faru lokacin zaben 2015
  • Akande ya ce Buhari ya yi alkawarin zaben Tinubu matsayin mataimakinsa amma ya gaza cika alkawarin
  • Wadannan bayani na cikin littafin rayuwar Bisi Akande mai suna “My Participations”, da aka kaddamar ranar Alhamis

Lagos, Nigeria - Tsohon Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Cif Bisi Akande, ranar Alhamis, 9 ga Disamba, ya bayyana yadda Shugaba Buhari ya kasa cika alkawarin da yayi wa Tinubu na zabensa matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2015.

Thisday ta ruwaito cewa Akande ya bayyana hakan cikin littafin rayuwar Bisi Akande mai suna “My Participations”, da aka kaddamar ranar Alhamis a Legas.

Akande yace bayan alkawarin da Buhari yayi, daga baya ya canza baki yace shi ba haka ya fadi ba, kawai "cewa yayi zai so suyi aiki tare."

Kara karanta wannan

Akande: Tsohon Shugaba Obasanjo ya karya kowa, Tinubu kadai ya gagare sa a 2003 – Buhari

Akande ga Buhari
Ka yi alkawarin zaben Tinubu matsayin mataimakinka amma ka saba: Akande ga Buhari Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Wasu sun budewa Buhari wuta

Bisi Akande ya bayyana cewa wasu Gwamnonin Arewa sun budewa Buhari wuta inda suka ce ba zai yiwu Musulmi da Musulmi su zama Shugaba da mataimaki ba.

Daga baya, Buhari ya bukaci Tinubu ya gabatar da sunayen mutum uku daga yankin Yarabawa don ya zabi daya.

Wannan saba alkawari da Buhari yayi ya baiwa Tinubu haushi, hakan yasa ya bar Abuja ya koma Legas.

Bayan hakuri da lallashin da aka yiwa Tinubu, daga baya yace a zabi Osinbajo matsayin mataimakin Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel